Hukumar ilimin bai daya na nuna hazaka a Adamawa
Hazikancin jami’an hukumar kula da ilimin bai daya na bunkasa karatun Firmare a Adamawa, musammman ganin yadda Mohammed Hassan Toungo lke jan ragamar hukumar shi ya sa ake da tabbacin ingantuwar al’amura. Bayan shelar matakan gaggawa na farfado da Ilimi shi ne Ilimin Firamare. Kafin nadin Mohammed Hassan Toungo a matsayin Shugaban Hukumar Ilimin bai […]
Hazikancin jami’an hukumar kula da ilimin bai daya na bunkasa karatun Firmare a Adamawa, musammman ganin yadda Mohammed Hassan Toungo lke jan ragamar hukumar shi ya sa ake da tabbacin ingantuwar al’amura.
Bayan shelar matakan gaggawa na farfado da Ilimi shi ne Ilimin Firamare. Kafin nadin Mohammed Hassan Toungo a matsayin Shugaban Hukumar Ilimin bai daya na Jihar Adamawa, an kona makaratun firamare da ke kananan hukumomi bakwai na shiyyar Adamawa ta Arewa. Wasu daga cikin makarantun firamaren an kona su kurmus. Abin babu kyawun gani in ka ziyarci wasu daga cikin makarantun da aka yi wa ta’adi. An kashe wasu malamai, an kuma kama wasu ’yan makaranta aka tilasta su shiga kungiyar Boko Haram. lyayen yaran kuma, mazansu da matansu ko dai an yi musu kisan gilla ko an gudu da su zuwa dajin Sambisa. Makarantun firamare da ke kananan hukumomi 14 da suka rage su ma ba su tsira ba. Ko dai ambaliyar ruwa ya shafe su ko an yi watsi da su ko rashin kula da su ya sa sun lalace, wato kananan hukumomin Toungo, Ganye, Jada, Mayo-Belwa, Demsa, Numan da Lamurde da Guyuk da Shelleng da Song da Fufore da Girei da Yola Ta Arewa da kuma Yola Ta Kudu. Ana karantar da wasu yaran a karkashin bishiyoyi. Wasu ana karantar da su a azuzuwa masu yoyo.
Shugabancin Mohammed Hassan Toungo ya sauya duk al’amura kasancewarsa kwararren malami, Babban Mai Koyarwa a Kwalegin Ilimi ta Tarayya da ke Yola, inda ya dukufa ka’in da na’in wajen gyare-gyaren makaratun, samar da kujeru da tebura, domin yin karatu a tsanaki. Ya shiga rangadi na makarantun wurjajan duk inda ya je yana bada umurnin aiwatar da abin da ya dace.
Ba zama yake a a ofis ba, domin na tuna lokacin da gobara da lamushe Makarantar Firamare Ta Abubakar Namtari da ke Yola ya ziyarci Makarantar kashegari ya duba ta’adin da gobarar ta yi. Tare da hadin gwiwar Shugaban karamar Hukumar Yola ta Kudu Hon. Abubakar Dauda, Toungo ya ba da umurnin sake gina azuzuwan da suka kone, tare da samar da litattafai ga dakin karatu na makarantar da ya kone. Mohammed Hassan Toungo yana son ganin an kawo sauyi mai ma’ana wajen bayar da Ilimin Firamare. Yana yin abin da Mai Girma Gwamnan Jihar Adamawa, Seneta Muhammadu Umaru Jibrilla Bindow yake so yara su taso suna da ilimi irin na zamani.
Misali, an bude Cibiyar Fasahar Sadarwa ta Zamani a Makarantar Firamare Ta Gwadabawa da ke Jimeta, tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta. Ana sa ran fadada cibiyar zuwa sauran makarantun firamare na jiha. Kamfanin Mai da Gas na Oando ya dauki nauyi a matsayin nasa gudumawar ga al’umma. An gyara sassa 52, inda kowane da ke da azuzuwa uku da Ofis da kuma baranda. An kuma gyara sashe-sashe 52 na ingantattun makewayi. An kuma samar da kujeru dubu 41,530 na ‘yan aji uku aka kuma rarraba wa makarantu.
Haka nan an sayi tebura da kujerun malamai dari shida da ashirin da takwas aka rarrabawa makarantu hamsin da biyu. Ya zuwa yanzu makarantu dari da goma sha daya aka gyara. Dadin dadawa an gayra afisoshin sashen gudanarwa guda biyu. Akwai kuma kayayyakin wassani na yara kanana (Nursery) kana an samarwa makarantun firamare sittin da shida naura mai amfani da kwakwalwa (computer). A yanzu haka Hukumar Bada Ilimi Bai Daya ta kasa ta ba da amincewa na ayyuka na 2,015 tuni Gwamnatin Jihar Adamawa ta ba da nata kason.
Hukumar karkashin jagorancin Mohammed Hassan Toungo ta kammala tanade-tanade tare da Kwalejin Ilimi Ta Tarayya da ke Yola, inda kuma ta rattaba hannu kan yarjejeniya ta horar da malamai 6,452 da suka warwatsu a kananan hukumomi 21 na jiha, wadanda ba su samu kwarewa a aikin malanta ba. Babban abin damuwar kowane mai kishin Jihar adamawa da Najeriya baki daya, tabbas zai so a ce irin wannan gagarumar nasara da Mohammed Hassan Toungo da sauran hazikan ma’aikatansa suk samu wajen bunkasa ilimi lallai a yi kokarin tabbbatar da dorewarta, t ayadda wasu ma za su yi koyi. Don haka Gwamna Jihar Adama alhaji Muhammad Bindo ya kara musu kwarin gwiwa da su ci gaba da wannan kkyakkyawan aiki.
Daga: Emmanuel Y. Kwache dan Jarida mai zaman kansa da ke sharhi kan al’amuran kasa a Titin mai lamba 1 Abaji Sabon Hanya, daura da Makarantar Fasaha ta Tarayya ta Mubi Tsangayar Yola da ke bunoklang Karamar Hukumar Girei, Jihar Adamawa, Nigeria
[email protected] [email protected] 08087721703, 08140022647.