Hukumar INEC ta dakatar da ‘yan takarar APC na Zamfara
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta dakatar da ‘yan takarar jam’iyyar APC daga neman takarar mukamai a babban zabe na 2019. Hukumar INEC ta sanar da cewa, matakin da ta dauka nada nasaba ne da rashin cika wa’adin da aka baiwa jam’iyyar na kammala fitar da ‘yan takarar jihar, kamar yadda dokar zaben kasar […]
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta dakatar da ‘yan takarar jam’iyyar APC daga neman takarar mukamai a babban zabe na 2019.
Hukumar INEC ta sanar da cewa, matakin da ta dauka nada nasaba ne da rashin cika wa’adin da aka
baiwa jam’iyyar na kammala fitar da ‘yan takarar jihar, kamar yadda dokar zaben kasar ta tsara.
Shugaban kwamitin gudanarwa na jam’iyyar Alhaji Lawali M.Liman ne ya sanar da dakatar da ‘yan takarar jam’iyyar APC na Zamfara.