Hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaben 2015

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta fitar da ka’idoji da jadawali da zaben shekarar 2015 a shekaranjiya Laraba.Da yake tattaunawa da Aminiya kan sanarwar wadda aka fitar a shafin intanet na INEC Lauya Ahmed Raji SAN, ya ce fitar da sanarwa ya sa yanzu wajibin ne jam’iyyun siyasa su bi ka’idojin da hukumar ta fitar. […]

Hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaben 2015
Hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaben 2015

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta fitar da ka’idoji da jadawali da zaben shekarar 2015 a shekaranjiya Laraba.
Da yake tattaunawa da Aminiya kan sanarwar wadda aka fitar a shafin intanet na INEC Lauya Ahmed Raji SAN, ya ce fitar da sanarwa ya sa yanzu wajibin ne jam’iyyun siyasa su bi ka’idojin da hukumar ta fitar.
Ahmed Raji wanda aka tuntuba ta tarho daga Kano, ya ce jadawalin ya kunshi lokacin zaben fidda-gwani da na mika sunayen ’yan takara da na canja su.
Raji wanda tsohon Kwamishinan Hukumar INEC ne a Jihar ya ce jadawalin wanda cika umarni ne na Dokar Zabe ta shekarar 2011, ana fata dukkan jam’iyyun siyasa su nazarce shi tare da kiyaye ka’idojinsa.
Ya ce sai dai wajibi ne jadawalin ya dace da tanade-tanaden tsarinmulki na 1999 da Dokar Zabe ta 2011, inda ya ce dokar zabe ba za ta ce kaza, jadawalin ya fadi akasi ba.
A karkashin jadawalin za a sanar da ranakun zabubbukan 2015 a ranar 1 ga Oktoba, yayin da 16 ga Nuwamba za ta kasance ranar fara kamfe din zabe a tsakanin jam’iyyun siyasa.
Ranar karshe ta mika fom din (CF 1) da (CF2) a hekdwatar INEC it ace 18 ga Disamba, 2014 domin zaben Shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta kasa, yayin da na zaben gwamnoni da ’yan majalisar jihohi aka kebe  1 ga Janairu, 2015 kamar yadda sashi na 31 (3) na Dokar Zabe ta 2010 (da aka yi gyara) ya tanada.
An keba ranar baje sunayen ’yan takarar Shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta kasa a ranar 13 ga Janairu, 2015, yayin da na gwamnoni da na majalisun jihohi zai kasance ranar 27 ga Janairum 2015.
Hukumar INEC ta ajiye 4 zuwa 11 ga Nuwamba domin karbar fom-fom din tsayawa takarar dukkan zabubbuka ga jam’iyyun siyasa.
Zaben Shugaban kasa da na Majalisar Dokoki ta kasa zai gudana a ranar 14 ga Fabrariru, 2015, yayin da na gwamnoni da majalisun dokoki na jihohi zai gudana a ranar 28 ga Fabrariru 2015.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi