Hukumar INEC ta haramta zuwa wurin kada kuri’a da wayar salula
Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ce za ta hana amfani da wayar salula wajen daukan hoto da bidiyo a rumfunan zabe. Mai magana da yawun hukumar, Malam Aliyu Bello ne ya tabbatar wa BBC da wannan labari, inda ya ce sun dauki matakin ne domin magance matsalar magudin zabe. A cewarsa, za su soma […]
Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ce za ta hana amfani da wayar salula wajen daukan hoto da bidiyo a rumfunan zabe.
Mai magana da yawun hukumar, Malam Aliyu Bello ne ya tabbatar wa BBC da wannan labari, inda ya ce sun dauki matakin ne domin magance matsalar magudin zabe.
A cewarsa, za su soma tabbatar da haramcin ne a zaben da za a yi a Jihar Osun gobe.
“Yin haka na daga cikin matakan da Hukumar Zaben ta dauka domin ta rage barnar da ake tafkawa a daidai lokacin da ake kada kuri’a. Hukumar na kokarin gano dabaru da salon yadda za a gudanar da zabe nagartacce ne,” inji shi.
Malam Aliyu ya ce bisa fahimtarsu, masu sayar da kuri’unsu suna kulla yarjejeniya ta yadda masu sayar da kuri’a za su nuna wa masu saye wata shaida da za ta gamsar da su cewa jam’iyyarsu mutum ya zaba gabanin su biya shi, don haka wannan dokar za ta magance wannan matsalar.
Jami’in na Hukumar Zaben ya yi kira ga jama’ar kasar nan su ba su hadin kai wurin ganin sun aiwatar da dokar ba tare da fuskantar matsaloli ba.
Ana zargin ’yan siyasar kasar nan da yin amfani da kudi wurin sayen katin zabe da kuri’u a yunkurin da suke yi na yin magudin zabe, ko da yake sun sha musanta zargin.