Hukumar INEC zata gudanar da sahihin zabe – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana wa wakilai masu lura da harkokin zabe daga Tarayyar Turai  EU cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC zata tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a kasar. Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da ayarin EU wanda daya daga cikin mamba ta Tarayyar Turai Maria Arena […]

Hukumar INEC zata gudanar da sahihin zabe – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana wa wakilai masu lura da harkokin zabe daga Tarayyar Turai  EU cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC zata tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da ayarin EU wanda daya daga cikin mamba ta Tarayyar Turai Maria Arena ta jagoranta suka ziyarci shugaban a fadar shugaban kasa.

Shugaba Buhari ya ce, ya tattauna da shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu a taron majalisar kasa akan batun gudanar da sahihin zabe Najeriya.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta