Hukumar JAMB ta dage jarrabawar gwaji da za a yi ranar Asabar
Hukumar shirya jarrabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantun Najeriya (JAMB/UTME) ta ce, a yau Alhamis ta rufe rijistar masu rubuta jarrabawar. Hukumar ta kuma ce, ta dage jarrabawar gwaji ta UTME da aka shirya yi ranar Asabar 23 ga Fabrairu 2019. Kakakin hukumar Dakta Febian Benjamin ya sanarwa da majiyarmu ta wayar tarho cewa, rijistar […]
Hukumar shirya jarrabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantun Najeriya (JAMB/UTME) ta ce, a yau Alhamis ta rufe rijistar masu rubuta jarrabawar.
Hukumar ta kuma ce, ta dage jarrabawar gwaji ta UTME da aka shirya yi ranar Asabar 23 ga Fabrairu 2019.
Kakakin hukumar Dakta Febian Benjamin ya sanarwa da majiyarmu ta wayar tarho cewa, rijistar jarrabawar da aka fara a ranar 10 ga Janairu 2019 an rufe yauAlhamis, an kuma dage jarrabawar gwaji aka shirya yi ranar Asabar saboda zaben shugaban kasa da za a yi ranar. Ya kuma ce za a sanar da ranar da za a yi nan gaba.
Dakta Febian ya ce, hukumar ta yi rijistar dalibai miliyan 1.8 wadanda zasu rubuta jarrabawar UTME ta 2019 wanda ake saran za a yi ranar 23 ga watan Maris 2019.