Hukumar Kiyaye Hadurra Ko Hukumar Tara Kudade?

Tun a cikin watan Fabrairun shekarar 1988, ta hanyar dokar soja ta 45 da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kirkiro Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC), sashe na II na kundin dokarta ya yi mata tanadin wasu daga cikin ayyaukanta kamar haka:- (a) Hana, tare da rage yawan hadurran ababen hawa a kan tituna. […]

Hukumar Kiyaye Hadurra Ko Hukumar Tara Kudade?
Hukumar Kiyaye Hadurra Ko Hukumar Tara Kudade?

Tun a cikin watan Fabrairun shekarar 1988, ta hanyar dokar soja ta 45 da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kirkiro Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC), sashe na II na kundin dokarta ya yi mata tanadin wasu daga cikin ayyaukanta kamar haka:- (a) Hana, tare da rage yawan hadurran ababen hawa a kan tituna. (b) Kawar da duk wani abu daga kan tituna da ka iya kawo cikas cikin zirga-zirgar ababen hawa. (c) Ilmantar da direbobi da masu motoci da sauran masu amfani da ababen ko tituna, a kan yadda za su rika amfani da tituna yadda ya kamata. (d) Samar da kyakykyawar kula kuma a kan lokaci ga mutanen da ka hadu da hadurra kan tituna. (e) Gudanar da bincike a kan hadurran da sukan faru. (f) Tabbatar, tare da tantance da kuma takaita gudun kowace mota a kan hanyoyinmu. (g) Hada kai da hukumomi da kungiyoyi da dukkan wadanda suke cikin kula tabbatuwar kiyaye hadurra da sauran abubuwan ki a kan titunanmu.
Idan ka bi sawun wadannan aikace-aikace za ka taras sun kara kunsar yadda za a ba da lasisin tuki da kula da lafiyar ababen hawa da tsarawa da buga lambobin ababen hawa, motoci/babura, sannan sai ka yi batun tara kudaden shiga daga masu ababen hawa da suka zama masu kunen kashi, domin tunda dai aka ce ga doka, to, kuwa lallai a samar da hukunci a kan wanda ka karya ta, kodayake yin hukuncin, ba  shi ne a`ala ba, sai inda ya zama tilas.
Amma ita Hukumar FRSC, ka iya cewa babban aikin da ta fi mayar da hankali a kai shi ne kawai yadda za ta tara wa gwamnatin tarayya kudaden shiga, alhali tana ji tana gani afkuwar hadurra a kan titunan kasar nan suna kokarin su gagare ta shawo kansu, sai dai a duk lokacin da aka yi hadurran za ka ji jami`anta kan dora fakuwarsu a kan tukin ganganci ko rashin lafiyar ababen hawa, amma ba za ka taba jin su suna danganta afkuwarsu a kan rashin kyawawan hanyoyi da ya zama ruwan dare a kasar nan. Abin da ya kai matsayin da masu kula da al`amurran da ka je su zo a kasar nan na cewa mutanen da suke mutuwa ta hanyar hadurran ababen hawa duk shekara sun zarta wadanda suke mutuwa ta hanyar mummunar cutar nan ta ‘Aids’.
A bana, an  kiyasata Hukumar FRSC za ta tara kudaden shiga har sama da Naira biliyan hudu. Batun tara kudaden shigar ne ya kawo ni a kan hukuncin da Mai shari`a James Tsoho na babbar kotun Jihar Legas ya yanke a cikin makon jiya, bayan ya saurari karar da wani Lauya mai zaman kansa, Barista Emmanuel Ofoegbu, ya shigar a ranar 30-09-13, inda yake kalubalantar aniiyar Hukumar FRSC din na tilasta wa masu ababen hawan kasar nan da lallai-ilallah da su canja lambobin ababen hawansu daga nan zuwa ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa, canjin lambobin da ba sai an fada ba, zai yi matukar kara nauyaya aljihun Hukumar. A da dai Hukumar ta tsaida ranar 1 ga watan Oktoban bara, don tilasta sabbin lambobin, amma sai ta daga zuwa 1ga watan Yunin bana.
A cikin waccan kara, Barista Emmanuel ya fada wa kotun cewa a duk dokokin da suka kafa Hukumar FRSC, ba inda aka yi mata tanadin da tilasta wa masu ababen hawa su canja lambobin ababen hawansu, don haka ya nemi kotun da ta taka wa Hukumar burki a kan wannan yunkuri. Ya tunatar da kotun cewa tsofaffin lambobin ababen hawan da ake amfani da su yanzu, an bayar da su ne bisa tanadin dokar ababen hawa ta shekarar 2004. Ya ce da wannan doka da dukkan sauran dokokin kasa, hatta tsarin mulki, ba inda aka yi tanadi ga Hukumar ta tilasta wa masu ababen hawa su canja lambonin ababen hawansu.
Da yake yanke hukunci, Mai shari`a Tsoho, ya tabbatar da da`awar mai kara na cewa Hukumar ba ta da hurumin ta tilasta wa masu ababen hawa su canja lambobin ababen hawansu da wasu sababbi a cikin wani kayyadajjen lokaci, duk kuwa da cewa ikonta ne ta tsara sannan ta buga lambobin ababen hawa don amfanin masu ababen hawan. Don haka sai ya bayyana yunkurin Hukumar a kan haka tamfar kokarin wuce makadi da rawa ne.
Da take mayar da martini a kan hukuncin kotun, Hukumar FRSC, ta hannun kakakinta, Mista Jonah Agu, cewa ta yi ta fahimci hukuncin kotun, kuma ta yi na`am da shi, don hukuncin ya tabbatar da cewa ita ke da ikon tsara da buga lambobin ababen hawa, amma abin da kawai ta rasa a hukuncin shi ne tsaida ranar da za ta tilasta wa masu ababen hawa da lallai sai sun yi amfani da sabbin lambobin, abin da ya ce yanzu za ta daukaka kara don ta samu ikon yin haka. Hukumar kuma ta fadi cewa ba ita ta kayyade ranar daina amfani da tsofaffin lambobin ba, zaman Kwamitin hadin guiwa na Hukumomin tara kudaden shiga na jihohi da babban birnin tarayya Abuja shi ya yanke hukuncin wa`adin.
Komai dai zai biyo baya, a cikin daukaka karar da Hukumar za ta yi, abin da ke gaskiyar al`amari a tilasta wa masu ababen hawa su sake lambobin ababen hawansu a irin wannan lokaci ko kadan bai dace ba, kuma zalunci ne da rashin tausayin talakawa. A kullum nikan tambayi kaina me ke cikin lambar abin hawa da ya wuce shaida? Har gobe, ina ganin lambar motar Sarkina Sarkin Katsina mai martaba, Alhaji Sa Usman Nagwaggo (Allah Ya gafarta masa) mai KT 1 a wata zungureriyar motarsa ja, a zuciyata.  
Wadannan lambobin na yanzu da ba su da wani inganci duk da kamfen din da Hukumar FRSC take na cewa suna da wasu tanade-tanaden tsaro, ta yadda wai duk inda mota ta shiga za a ganta duk zance ne da neman  a karbi kudaden `yan kasa, don kuwa har yanzu ban taba jin jami`an Hukumar FRSC din sun ce sun taba gano wata mota da aka sata ta na`urarsu ba. Don haka don a karbi kudaden jama`a kawai ake son tilasta musu. A nan ya zama wajibi ga `yan Majalisun Dokoki na kasa da Gwamnatin tarayya da lallai su hana Hukumar ta FRSC tilasta wadannan sabbin lambobin ababen hawa na caka ga `yan kasa. Yanzu kuma ya kamata su dauki mataki, sai dai idan Hkumar tara kudaden shiga ake so a mayar da Hukumar FRSC, ba ta kare hadurra ba.