Hukumar Kiyaye Hadurra ta jaddada muhimmancin amfani da bel a kujerar baya

A wani sabon kokari na ceto rayukar direbobi da fasinjoji da ke amfani da hanyoyi a Najeriya, jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC) sun sake kaddamar da kamfe din wayar da kan jama’a kan muhimmancin amfani da bel a kujerar baya a yayin tafiye-tafiye a motoci a sassan Najeriya. Lokacin da Hukumar FRSC ta […]

Hukumar Kiyaye Hadurra ta jaddada muhimmancin amfani da bel a kujerar baya
Hukumar Kiyaye Hadurra ta jaddada muhimmancin amfani da bel a kujerar baya

A wani sabon kokari na ceto rayukar direbobi da fasinjoji da ke amfani da hanyoyi a Najeriya, jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC) sun sake kaddamar da kamfe din wayar da kan jama’a kan muhimmancin amfani da bel a kujerar baya a yayin tafiye-tafiye a motoci a sassan Najeriya.

Lokacin da Hukumar FRSC ta fara kamfe tare da tilasta amfani da bel a kujera a Janairun shekarar 2003, masu amfani da hanyoyi da dama sun yi maraba da shirin tare da samun mabambantan ra’ayoyi. Direbobi da fasinjoji da dama sun nuna tsoro, wasu kuma sun nuna shakka da damuwa, yayin da wasu da dama suka yi watsi da hakan, suna masu cewa wannan daya daga cikin tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya da ba za su dore ba.
Sai dai a lokacin da jami’an hukumar suka tsunduma a aiki, sun kunyata wadanda suke caccakarta. ’Yan Najeriya sun kasance masu kula da tsaron rayukansu a yayin tuki.
Mutane da dama da suka tattauna da Aminiya kan alfanun sanya bel a mota sun yarda cewa an ceto rayuka da dama sakamakon amfani da bel , yayin da aka yi asarar wasu da dama saboda kin bin dokar kare lafiyar matafiyan. Sun nuna mamaki kan yadda galibin ’yan Najeriya suke adawa da duk wani bakon abu ko sauyi, komai amfanin da ake ganin za su kawo.
“Abin takaici ne ganin yadda ’yan Najeriya suke koyon abu ta hanyar tilas. A wannan bangare duk da cewa akwai adawa, a karshe Hukumar FRSC ta samu gagarumar nasara, inda direbobi da fasinjoji suka rika mika musu wuya duk da cewa cewa ba cikin dadin rai ba,” inji su.
Bincike ya nuna cewa ga masu tukin motoci, tsoron jami’an hukumar kiyaye hadurra tilas ne. Kuma an gano masu motoci da dama da motocinsu ba su da bel an tilasata su sanya musu a lokacin da umarni da bel ya fara aiki, kuma batun ya zamo ruwan dare game duniya.
Kamfanoni da hukumomi ba a bar su a bay aba, a gwagwarmayar kiyaye hadurra a kan hanyoyi, inda amfani da bel ya zamo wani tsari na kamfanoni da dama. Hukumomi da kamfanoni da dama sun tilasta wa ma’aikatansu sanya bel a kowane lokaci suke tuki don gudanar da hidimomin kamfani.
daya daga cikin wadannan kamfanoni shi ne kamfanin Jarander Serbices Nigeria Limited, inda kamfanin ya fito da tsarin shelar ‘Ba bel , Ba shiga, Ko fita.’ A kamfanin Jarander, wannan tsari ana matukar sanya ido a kansa tare da binsa sau da kafa. Domin a tabbatar da bin wannan ka’ida, an umarci direbobi a koyaushe su sanya bel su kafi su fara tafiya da motocinsu a kowane lokaci, tare da tunatar da fasinjojinsu su ma su yi haka. Su kuma jami’an tsaro an umarce su kan su rika sanya ido da duba motocin kamfanin don tabbatar da ana kiyaye wannan ka’ida.
A shafib yanar gizo na Hukumar FRSC kan Umarni da Sanya Bel a Motoci a Najeriya da Aminiya ta duba, ta gano cewa kamfanin Jarander Serbices ya bayar da umarnin cewa: “Jami’an tsaro su hana kowace mota bari ko shiga harabar kamfanin har sai dukkan mazauna motar sun bi wannan umarni. Kuma a cikin harabar ko wuraren da ake gudanar da aikin kamfanin, aikin jami’an kula da lafiya da na sufabaizoji da kuma manyan jami’ai da suke wurin ne su tabbatar kowa a kamfanin da yake da mota ya sanya bel a motarsa ko motarta.”
Wasu kamfanoni ma da dama sun bi sahun irin hakan, inda suke tilasta wa ma’aikatansu sanya bel a kujera yayin tuki a harabobinsu.
Duk da dimbin nasarorin da jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra suka samu wajen saisaita mahaya ababen hawa su rika amfani da bel a kujera, bincike ya nuna an fi mayar da hanakali ga direbobi da fasinjojin da ke gaban mota. Su kuwa fasinjojin da ke bayan mota ba su dauki sanya bel a kujerar da muhimmanci a lokacin da suke tafiya ba.
Wani mai motar haya a Jabi da ke Abuja, Mista James Okwuchukwu da yake tattaunawa da Aminiya ya nuna matukar mamakinsa ganin cewa fasinojin da ke kujerun bayan mota za a tilasta musu amfani da bel yayin da suke tafiya a cikin mota. Ya jajirce cewa wadannan fasinjoji ba su tattare da wani hadari na fadowa daga abin hawa koda an yi hadari.
“Wace irin doka ce wannan? Me zai sanya a tursasa wa fasinjojin da ke zaune a bayan mota sanya damara? Wannan ba ma matsin lamba ba ne kawai, yana ma tattare da hadari, tunda fasinjojin na zaune dab-da-dab da juna. Wannan ba daya yake da na gaban mota ba. Ina ganin Hukumar FRSC ta bullo da wannan tsarin ne saboda ba ta san wani abu da ya kamata ta aiwatar ba,” inji shi.
Sai dai wani mai motocin haya Cif Kolawole Olusegun, bai yarda da ra’ayin Okwuchukwu ba, inda ya ce fasinjojin da ke zaune a bayan mota na tattare da hadari iri daya da wadanda ke zaune a gaba.
“Shin kuna jin cewa wadanda suka kera ababen hawa shirme suka yi wajen kara damarun a kujerun baya? Na kasa gane yadda ’yan Najeriya ke da wuyar sha’ani wajen fahimta da aikata abin da yake daidai,” inji Olusegun.
Damuwa da hadarin da ke tare da kin bin wannan doka, ya sanya Hukumar FRSC ta himmatu ka’in-da-na’in wajen fadakarwa kafin fara aiki da dokar a Janairun 2015. Wasu takardun bayanai da wakilinmu ya samu, Hukumnar FRSC ta nuna yadda jami’inta suka jajjirce wajen cimma Yarjejeniyar Accra a shekarar 2015, inda aka kudurin aniyar rage munanan hadurra da kashi 50 cikin 100; don haka aka himmatu wajen fadakar da al’umma game da tilasta amfani da bel ga daukacin masu tafiya a motoci.
Hukumar FRSC ta ce, ta yanke wa’adi mai tsawo ne don fadakarwa ta yadda kowane dan Najeriya, zai gane.
Jami’in fadakarwa na hukumar, Mista Imo Etuk, da yake yi wa wakilinmu bayani kan amfani da damara kujera ga fasinjoji baya, ya ce: “A halin yanzu, Hukumar FRSC, ba ta yanke ranar fara amfani da damara a kujerar baya ba, saboda fadakarwa na daya daga cikin muhimman manufofinmu, don saisaita masu motoci kan yadda za su rika tafiyar da harkoki a kan hanyoyi. Wannan yana cikin ka’idodjin aiki da aka bijiro mana da su. Hukumar FRSC a koyaushe ta dogara ne kan fadakarwa da ilimantarwa ga al’umma don tafiya a kan hanyoyi ba tare da hadari ba. Idan ba a manta ba, an yi ta tatttaunawa da shirya tarurruka a Abuja da Legas da masu ruwa da tsaki a harkar sufuri, kuma kafin mu fara kamfe din makala wa motoci na’urorin kayyade gudu a daukacin motoci da ke kasar nan.
A wadannan tarurruka mun bayar da dama ga abokan huldarmu, wadanda suka hada da Hukumar Tantance Nagartar Kayayyaki (SON) da kuma wadannan fadakarwa don share fagen fara aiki da na’urar a ranar 1 ga Yunin 2015.”
Ya kara da cewa: “Kuma a kan sanya bel a kujerar baya, inda muke amfani da kafafen watsa labarai da suka hada da talabijin da rediyo da tattaunawa a jaridu da tarurruka a tashoshin mota, da kai ziyarar ban girma (ga rukunonin jama’a), wadannan duk suna daga cikin dabarun da muke amfani da su don gnain ’yan Najeriya sun fahimci muhimmancin amfani da bel a kujerun baya a motoci lokacin da suke tafiya, al’amarin da ya kasance tanadin doka ne, kamar yadda yake kunshe a sashi na 126 (1) Dokar Daidaita Hada-Hada a Hanyoyin kasa ta shekarar (2012), wadda ta yi daidai da manufar Majalisar dinkin Duniya ta 4, a matakin shekara 10 da aka dauka don kiyaye hadurra.”
“Idan ka dubi dokar amfani da manyan hanyoyi, za ka fhaimci cewa amfani da bel ga daukacin mutane da ke cikin motoci yana rage illar jin rauni da ake samu yayin da aka yi hadari da kashi 50 cikin 100. A dunkule, manufar amfani da bel al’amari ne mai fa’ida ga kowa. Irin wannan fadakarwar ta yi daidai da ta tilasta amfani da bel na kananan yara ga iyaye. Ya kamata mu kula da cewa kowane karamin yaro za a rika sanya masa bel a kujerar baya, har sai ya/ta kai shekara 12 kafin a fara dora shi/ta a kan kujerar gaba, inda zai sanya bel ya/ta zauna yadda ya dace.”
Etuk ya ce a matsayin hukumarsa na ja-gaba wajen kiyaye hadurra da kula da ababen hawa a Najeriya, Hukumar FRSC ta sake daura bel wajen cusa wa mutane managartan dabi’u don kiyaye hadurra a tsakanin masu amfani da ababen hawa a hanyoyin kasar nan. Ya ce Hukumar FRSC tana tsaye wajen cimma manufofin da za su shawo kan munanan hadurran da ake fama da su a hanyouyin.
Ya ce akwai bukatar a cusa managartan dabi’u ga jama’a, don tabbatar da tsare dokar kiyaye hadurra.
A wasu takardun bayanai da wkailinmu ya samu daga Hukumar FRSC, an ce: “Akwai bukatar masu motoci su tabbatar da cewa suna da bel a kujerun baya da na gaba. Don a tabbatar da cewa ana bin wannan doka sau da kafa, don a samu daidaituwar al’amura a kan manyan hanyoyin kasar nan.”
Wadannan takardun bayanai, sun bayyana cewa bel da majanyin karamin yaro na rage hadarin da ke tare da matse wa gaban ababen hawa da jin mummunan rauni idan aka yi hadari. Kuma suna tattara karfin bugun hadari a sassan jiki masu karfi, sannan su hana a jefo mutum waje daga cikin mota da bayar da kariya daga samun raunuka ga wadanda ke cikin motocin.
Alal misali, a yayin karo na gaba da gaba, fasinjojin da ba su sanya bel ba, kuma suke zaune a kujerun baya za a iya jefo su waje yayin da aka yi karo, su kuma yi karo da sauran mutanen da ke cikin motocin.
“Fasinjojin bayan motoci, wadanda ba a ba su kariya ba, suna tare da jefa sauran mutanen da ke gabansu cikin hadari. Shi kuwa wanda ya sanya bel , zai zauna manne a kujerarsa, ta yadda za a rage yawan wadanda hadarin zai jikkata. Don haka amfani da bel ga fasinjojin da ke zaune a kujerun baya na da matukar muhimmanci,” kamar yadda yake kunshe a cikin takardun bayanan.