Hukumar kula da masu jiragen ruwa ta gyara makarantun Borno
A ranar Alhamis 24 ga Agusta ne Hukumar Kula da Masu Harkar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (Nagerian Shipper’s Council) ta mika makarantun sakandare uku da ta gyara ga gwamnatin Jihar Borno a matsayin wani bangare na aikin tallafa wa jama’a na kamfanin. Makarantun uku suna daga cikin makarantun da kungiyar Boko Haram ta lalata […]
A ranar Alhamis 24 ga Agusta ne Hukumar Kula da Masu Harkar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (Nagerian Shipper’s Council) ta mika makarantun sakandare uku da ta gyara ga gwamnatin Jihar Borno a matsayin wani bangare na aikin tallafa wa jama’a na kamfanin. Makarantun uku suna daga cikin makarantun da kungiyar Boko Haram ta lalata a Jihar Borno. Majalisar ta ce ta dauki nauyin gyara makarantun na gwamnati uku da ke birnin Maiduguri ne a lokacin da Babban Sakatarenta kuma Shugabanta, Hassan Bello ya ziyarci Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima a watan Nuwamban bara. Kuma bayan bukatar da shugaban kungiyar ya mika ne gwamnatin Jihar Borno ta amince majalisar ta gyara Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Je-Ka-Ka-Dawo da ke Barikin Maimalari da Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Je-Ka-Ka-Dawo ta Maiduguri da kuma Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Je-Ka-Ka-Dawo ta Zajiri.
A cewar Daraktan Hulda da Jama’a na Majalisar, Balarabe Sama’ila wanda ya mika makarantun da aka gyara ga ma’aikatar ilimi ta jihar, majalisar ta takaita kanta ga gyara makarantu ukun ne da gwamnatin Jihar Borno ta zaba, kuma za ta gyara karin wasu idan aka zabo.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Borno, Musa Inuwa Kubo wanda ya wakilci gwamnatin jihar a wajen bikin ya nuna farin cikinsa kan gudunmawar da majalisar ta bayar.