Hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta inganta matakan tsaro

Hukumar  Kula  da  Tasoshin Jiragen  Ruwa  ta  Najeriya (NPA) ta ce  fashewar  bam  a  kusa da ita ba bai sa ta yi kasa  a gwiwa  wajen  tafiyar  da  harkokinta  na yau da kullum ba.Shugaban hukumar Malam Habib Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Legas a ranar Talata.Ya […]

Hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta inganta matakan tsaro
Hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta inganta matakan tsaro

Hukumar  Kula  da  Tasoshin Jiragen  Ruwa  ta  Najeriya (NPA) ta ce  fashewar  bam  a  kusa da ita ba bai sa ta yi kasa  a gwiwa  wajen  tafiyar  da  harkokinta  na yau da kullum ba.
Shugaban hukumar Malam Habib Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Legas a ranar Talata.
Ya ce tun daga lokacin da bam din ya tashi ne ya sanya hukumar ta inganta matakan tsaro, kuma har zuwa yau harkokinta na tafiya kamar yadda aka saba.
Ya ce  “Wurin da bam din ya tashi ba shi da nisa da wurinmu, amma hakan bai sa  mun yi  kasa  gwiwa  ba, inda muka tsaurara matakan shiga tashar jirgin ruwa da ke nan Legas.”
Ya ce kasancewar ana samun  cunkoson  motoci da suka hada da manya da kanana a wajen tashar,  jami’an tsaron da ke samar da tsaro a tashar sun kara jajircewa wajen ganin duk wani mai aikata ayyukan assha bai samu  nasara ba.
“Wannan ya sa a taron da muke yi lokaci zuwa lokaci na kasashen Afirka masu tashar jirgin ruwa, mukan fito da sababbin matakan tabbatar da tsaro a tsakaninmu, sannan mun kulla kyakkyawar alaka tsakaninmu da wadannan kasashe musamman ma wadanda suke kusa da Najeriya don su ci gaba da hulda da mu.” Inji shi.
Dangane miyagun ayyukan da ake aikatawa a tekun Najeriya wadanda suka zama barazana ga jiragen ruwan da suke shigo wa Najeriya sai ya ce,  duk  wannan ba aikin hukumarsu ba ne,  amma  sanin kowa  ne  wannan al’amari  ya  ragu, domin ba a jin duriyar  masu  aikata  miyagun ayyukan kamar da.
“Batun shigowa da muggan makamai cikin kasa ta tashan jirgin ruwa ya ragu sosai, domin dukkan tasoshin jiragen ruwan Najeriya da hadin gwiwar jami’an kwastan da na  sauran jami’an tsaro don tabbatar da duk jirgin da ya  sauke  kaya sai an yi  masa  binciken  kwakwaf.”
Ya ce tun daga lokacin da ya karbi ragamar mulkin  wannan tashar kawo yanzu, an kara samun yawaitar jiragen da ke shigowa ne, sabanin wadanda suke shigowa a da, kuma yanzu manya-manyan jirage na shigowa, kasancewar an kara tona teku, ta yadda babban jirgin ruwa zai ji dadin shigowa.