Hukumar Kwastam ta cafke masu fasa-kwauri a Katsina
Kwanturola Hukumar Kwastam mai kula da shiryyar Kaduna da Katsina Yerima Abubakar Gadam ya gargadi masu fasa kwauri a shiyyar cewa jami’insa za su sanya kafar wando daya da su.shaidawaKwanturola Yerima Gadam ya bayyana haka ne lokacin da yake bayani ga manema labarai a ofishinsa a ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce kasancewar […]

Kwanturola Hukumar Kwastam mai kula da shiryyar Kaduna da Katsina Yerima Abubakar Gadam ya gargadi masu fasa kwauri a shiyyar cewa jami’insa za su sanya kafar wando daya da su.
shaidawa
Kwanturola Yerima Gadam ya bayyana haka ne lokacin da yake bayani ga manema labarai a ofishinsa a ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce kasancewar shiyyar na da iyaka da kasar Nijar akwai hasashen karuwar fasa kwauri, don haka jami’ansa sun kara shiri don fuskantar wannan kalubale.
Kwantorola Yerima ya ce,”Hukumarsa ta kwace kayan fasa kwauri har sau 60
da kudin shigarsu zai kai Naira miliyan 73 da dubu 54. “A tsakanin 17 zuwa 22 ga Afrilu mun samu damar cafke motoci 8 dauke da buhunnan shinkafa 482 kuma mun kama katan 413 na kwayoyin Tramadol da Diclogun da dangoginsu da kwali 990 na Coldtime da kudinsu ya kai Naira miliyan 40 da dubu 977 da 640,” inji shi
Kwanturolan ya ja kunnen masu harkar fasa kwauri cewa “Ina kara nanata wa masu son gudanar da harkokin kasuwanci a tsakanin Najeriya da Nijar cewa kofofinmu a bude suke a gare su idan za su bin hanyoyin da doka ta tsara.”
Kwanturola Yerima Gadam ya ce, hukumarsa ta yi nasarar tara kudin shiga Naira biliyan daya da miliyan 325 a cikin wata uku na farkon bana, inda a dara na bara a daidai wannan lokaci da ta Naira biliyan daya da miliyan121.