Hukumar Kwastam ta gargadi masu fasa-kwauri

Hukumar Kwastam a shiyyar jihohin Kebbi Sakkwato da Zamfara ta ja kunnen masu shigowa da kaya kasar nan cewa su bi hanyoyin da suka dace, musamman wajen biyan kudin harajin shigo da kayansu, domin sana’ar fasa kwauri ba ta da riba, kuma ba ta arziki ba ce.Kwanturolan Hukumar mai kula da shiyyar, Sani Madugu ne […]

Hukumar Kwastam ta gargadi masu fasa-kwauri
Hukumar Kwastam ta gargadi masu fasa-kwauri

Hukumar Kwastam a shiyyar jihohin Kebbi Sakkwato da Zamfara ta ja kunnen masu shigowa da kaya kasar nan cewa su bi hanyoyin da suka dace, musamman wajen biyan kudin harajin shigo da kayansu, domin sana’ar fasa kwauri ba ta da riba, kuma ba ta arziki ba ce.
Kwanturolan Hukumar mai kula da shiyyar, Sani Madugu ne ya yi wannan jan kunne a lokacin  da yake ganawa da manema labaari a ofishin hukumar da ke Birnin Kebbi.
Sani Madugu ya ce, “Shigo da kaya ta barauniyar hanya, ko bata  suna da cin mutunci, ba za su tsoratar da mu ba, abin da ya fi wa masu yin haka, shi ne su canja salon shigo da kaya wajen bin ka’idoji.  Fasa kwauri ba ta da riba. Domin bayan asarar kaya, akwai yiwuwar zuwa kurkuku.”
Kwanturola ya ce, kamar yadda shugaban hukumar, Kanar Hameed Ibrahim Ali (mai ritaya) ya shelanta magance shigo da kaya ta hanyoyin da ba su dace ba, ma’aikatansu za su tashi tsaye wajen tabbatar da haka.
Sani Madugu ya ce, a makon jiya ma’aikatansu sun yi arangama da wadansu ’yan fasa kwauri a garin Geza da ke karamar Hukumar Kamba da ke Jihar Kebbi, inda ma’aikatansu suka harbi tayar wata motar ’yan fasa kwaurin, inda daga bisani ’yan fasa kwaurin suka ingiza wadansu matasa suka je wurin da ma’aikatansu ke zaune suka kone motoci biyu tare da lalata kayayyakin ma’aikatansu, inda ya  ce yanzu ’yan sanda suna bincike a kan lamarin.
Shugaban ya ce ba za su lamunci a yi musu zagon kasa wajen tara kudaden shiga ba, kuma dole su dakile fasa kwauri, saboda kudaden shiga sun yi karanci ga gwamnati, sakakamon faduwar darajar man fetur. Ya ce a cikin watan Janairun da ya gabatam hukumar ta tara sama da Naira miliyan 150.