Hukumar Kwastam ta kama kayayyaki na Naira miliyan 156 a Bauchi

Hukumar Kwastam Shiyya ta Hudu mai kula da jihohin Arewa maso Gabas da jihohin Benuwai da Filato da ke Bauchi, ta samu nasarar kame kayyakin da aka yi fasakwaurinsu ta barauniyar hanya da darajarsu ta haura Naira miliyan 156 a tsakanin Janairu zuwa watan Disamban nan. Babban Jami’i mai kula da shiyyar ta Zone D, […]

Hukumar Kwastam ta kama kayayyaki na Naira miliyan 156 a Bauchi
Hukumar Kwastam ta kama kayayyaki na Naira miliyan 156 a Bauchi

Hukumar Kwastam Shiyya ta Hudu mai kula da jihohin Arewa maso Gabas da jihohin Benuwai da Filato da ke Bauchi, ta samu nasarar kame kayyakin da aka yi fasakwaurinsu ta barauniyar hanya da darajarsu ta haura Naira miliyan 156 a tsakanin Janairu zuwa watan Disamban nan.

Babban Jami’i mai kula da shiyyar ta Zone D, Kwanturola Peters Olugboyega ne ya sanar da haka ga manema labarai a Bauchi. Ya ce, “Tsakanin watan Janairu zuwa Disamban bana, hukumarmu ta kama kayyakin da aka yi fasa kwaurinsu da suka kunshi shinkafa ’yar kasar waje da sabulai da tsoffin kayyakin sawa da taliya da wasu mugunguna dukan kayayyakin kudinsu ya kai Naira miliyan 156 da dubu 615 da 226,” inji shi.

Mista Peters ya ce “Mun kama shinkafa ’yar kasar  waje sau uku, na farko mun kama buhu 179 masu nauyin kilo 50, da kudinsu ya kai Naira miliyan 6 da dubu 627, mun kuma kama wata mota kirar J5 mai lamba KMC 855 DB dauke da buhunan shinkafar waje guda100, da kudinsu ya kai Naira miliyan 2 da dubu 520. sannan mun sake kama shinkafar waje buhu 130 da kudinta ya kai Naira miliyan 1 da dubu 872.”

Babban jami’in ya ce “A ranar 24 ga watan Nuwamban bana kuma mun kama katan-katan na sabulai mai suna ‘Eba-Soap’ guda 100, da kudinsu ya kai Naira milyan 1 da dubu 800.

Ya ce sauran kayayyakin da suka kama sun hada da taliya da kayayyakin gwanjo da aka yi fasakwaurinsu zuwa cikin kasar nan. Sai ya sha alwashin cewa ba za su zura ido suna kallon wadansu suna saba wa dokar shigowa da kayayyaki cikin kasar nan ba.

Mista Peters ya gargadi masu safarar kayayyaki ta barauniyar hanya su sauya halayensu. “Bari in yi amfani da wannan dama in gargadi dukan masu safarar kayayyaki ta barauniyar hanya, ya kamata su gane cewa kamar yadda suke sauya dabarun shigo da kayayyaki ta barauniyar hanya, haka mu ma muke sake sabunta dabarunmu na kama su. Don haka abin da ya fi kyautuwa a gare su shi ne su daina. A takaice dai a bi doka a zauna lafiya, ina son masu safarar kayayyakin nan su sani, yadda suke da hanyoyinsu, haka muke da hanyoyin magance su, saboda muna da hanyoyi sama da 101 na magance su. Za kuma mu ci gaba da fitar da tsare-tsaren dakile su,” inji shi.