Hukumar Kwastam ta kame kayayyakin Naira Miliyan 50 a Bauchi
Hukumar Kwastam ta kasa Shiyya ta Hudu da ke Bauchi ta kama motoci biyar dauke da kayayyakin da aka hana shigowa da su cikin kasar nan da kudinsu ya kai Naira miliyan 50 da dubu 237 da 400. Kwaturolan Hukumar a Shiyyar da ta kunshi jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Taraba da Bauchi […]
Hukumar Kwastam ta kasa Shiyya ta Hudu da ke Bauchi ta kama motoci biyar dauke da kayayyakin da aka hana shigowa da su cikin kasar nan da kudinsu ya kai Naira miliyan 50 da dubu 237 da 400.
Kwaturolan Hukumar a Shiyyar da ta kunshi jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Taraba da Bauchi da Gombe da Filato da kuma Benuwai da Nassarawa, Mista Peters Olugboyega ne ya sanar da haka lokacin da yake kewayawa da manema labarai kan kayayyakin a Bauchi.
Ya ce kayayyakin an kama su ne sakamakon bayanan sirri da aka samu a tsakanin watannin Agusta zuwa Satumban bana. Ya ce sun kama mota shake da taliyar waje katon dubu 1 da 963 a kan hanyar Potiskum zuwa Gombe, sai kuma jarkokin man gyada 780 na waje a cikin motar.
Kwanturolan ya ce kayayyakin sun saba wa dokar hana shigo da kayayyakin abinci sashe na hudu na Hukumar Kwastam sakin layi na 45 na dokar shekarar 2004 da aka yi wa gyaran fuska.
Kuma ya ce sun kama wata mota kirar Marsandi a kan hanyar Bauchi zuwa Jos shake da shinkafar kasashen waje buhu 300, inda aka kunshe su a cikin buhunan BUA. Ya ce sun kuma kama motoci uku shake da gwanjo a hanyar Bauchi zuwa Kano.
Mista Peters ya ce wadannan kayayyaki Gwamnatin Tarayya ta hana shigo da su, don babu dalilin da zai sa a shigo da su. Sai ya gargadi masu fasa kwauri su guji aikata hakan, in suka ki jami’ansu a shirye suke, su kama su kuma duk wanda suka kama za su gurfanar da shi a kotu don fuskantar hukunci.
Ya gode wa Shugaban Hukumar ta kasa, Kanar Hamidu Ali (mai ritaya) bisa yadda ya ba su damar gudanar da aikin yaki da fasa -kwauri a kasar nan ba tare da nuna sani ko sabo ba.
Haka ma Hukumar Kwastam a Jihar Ogun ta ce jami’anta za su rika bi cikin gidaje da dakuna da shaguna da rumbunan adana kayayyaki da sauran kantuna, domin su rika kwace shinkafar da aka shigo da ita daga waje ba bisa ka’ida ba.
Kwamaturolan Shiyyar, Micheal Agbara ne ya bayyana haka, inda ya ce a cikin watan da ya gabata jami’ansa sun dakile ayyukan fasa-kwauri tare da samar wa Gwamnatin Tarayya makudan kudin shiga.
Ya yi wannan jawabi ne ga manema labarai a kan iyakar Idiroko a yayin da yake bayyana sabon salon aikin hana fasa-kwauri da za su fara ba da dadewa ba.
Daga nan ya ce dirar mikiyar da za su fara a gidaje da kantuna da ma’ajiyar kaya tana da madogara daga dokar da ta kafa aikin Kwastam, ba wai da rana-tsaka suka yi nufin yin wannan gagarumin aiki na kwacen shinkafa da aka yi fasa-kwaurinta ba.