Hukumar kwastam ta lalata kayan Naira miliyan 50 a Jihar Oyo
Ranar Litinin ne rundunar kwastam ta Jihohin Oyo da Osun ta lalata katon dubu 10 na daskararrun naman talo-talo da aka kiyasta kudinsu ya kai fiye da Naira miliyan 48, wanda jami’an rundunar suka kama ranar Juma’a da ta wuce. Kwamandan rundunar, Kwanturola Richard Oteri, shi ne ya jagoranci wakilan rundunonin tsaro na ‘yan sanda […]

Ranar Litinin ne rundunar kwastam ta Jihohin Oyo da Osun ta lalata katon dubu 10 na daskararrun naman talo-talo da aka kiyasta kudinsu ya kai fiye da Naira miliyan 48, wanda jami’an rundunar suka kama ranar Juma’a da ta wuce.
Kwamandan rundunar, Kwanturola Richard Oteri, shi ne ya jagoranci wakilan rundunonin tsaro na ‘yan sanda da NDLEA da NAFDAC zuwa kauyen Arapaja da aka haka babban rami aka binne, bayan an barbada musu guba, sannan aka cinna musu wuta.
Kafin a gudanar da aikin, sai da Kwanturola Richard ya nuna wa ‘yan jarida buhuna 107 na ganyen tabar wiwi da jami’ansa suka kama a cikin wata motar bas a garin Igboora. Ya ce jami’an nasa sun kama motar ne safiyar Litinin.
A daidai wannan lokaci, a ofishinsa, Kwanturola Oteri, ya mika buhunan ga Kwamandan rundunar yaki da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta Jihar Oyo, Uwargida Omobolade Faboyede.
Duk wadannan kaya da aka kama, a lokuta daban-daban a cikin mako daya, babu mutum ko daya da aka yi nasarar kamawa a matsayin wanda ya mallake su. Sai dai a cikin motar an gano wasu takardu dauke da sunayen mutanen da suka mallake ta, wanda hakan zai taimaka wajen gano mutane da suka tsere a lokacin da jami’an kwastam suka tare su a cikin daji, domin bincike.
“Wadannan nasarori da muke samu, sun biyo bayan irin tashi tsayen da Kwanturola Janar Abdullahi Dikko Inde yake yi wajen wadata mu da ingattattun kayan aiki, kamar motocin shiga cikin kwazazzabai da bindigogi kirar AK47. Muna sane da irin hanyoyin da masu fasa kwauri suke dauka, musamman masu ba su labarin shirinmu da daukar manyan bindigogi a hannunsu da barayin hanyoyin da suke budewa da makamantansu, wanda mun riga mun karya lagonsu a Jihohin Oyo da Osun. Muna bukatar karin hadin kai a tsakaninmu da sauran rundunonin tsaro domin yaki da miyagun iri”. Inji Kwanturola Oteri.