Hukumar Kwastam ta raba tallafi ga ’yan gudun hijira

Sakamakon yawan rikicin makiyaya da manoma da kuma ambaliyar ruwa, Hukumar Kwastam a Jihar Adamawa da Taraba ta ba da tallafi ga ’yan gudun hijira da  wadanda ambaliyar ta shafa a karamar Hukumar Numan da ke Jihar Adamawa. Kayan tallafin sun kunshi buhunan shinkafa 532 da gwanj, kulli 139 da man gyada da lemun kwali, […]

Hukumar Kwastam ta raba tallafi ga ’yan gudun hijira
Hukumar Kwastam ta raba tallafi ga ’yan gudun hijira

Sakamakon yawan rikicin makiyaya da manoma da kuma ambaliyar ruwa, Hukumar Kwastam a Jihar Adamawa da Taraba ta ba da tallafi ga ’yan gudun hijira da  wadanda ambaliyar ta shafa a karamar Hukumar Numan da ke Jihar Adamawa.

Kayan tallafin sun kunshi buhunan shinkafa 532 da gwanj, kulli 139 da man gyada da lemun kwali, wadanda aka raba wa ’yan gudun hijirar da ke garuruwan Bolki da Gon da Nzumosu da kuma Yanga.

Kwamandan Hukumar Kwastam a Jihar Adamawa, Kamaludeen Olumoh ya ce an ba da tallafin ne sakamakon umartarsu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta hanyar shugabansu Hamid Ali, cewa su rika kai wa ’yan gudun hijira, musammam na Arewa maso Gabas tallafi.

Wanda ya wakilci Kwamandan Kwastam a Jihar Adamawa a yayin raba kayan, Bappa Usman ya ce suna iya kokarinsu domin kama masu shigo da kaya ba bisa dokokin kasa ba. Ya jinjina wa kananan ma’aikatansu masu kokarin gano wasu ayyuka da ke faruwa a jihar, wadanda ba a kan tsari ba gami da kama masu aikata laifuffuka. Ya ce suna kara himma domin ganin cewa sun kama masu shigo da kayan da suka keta dokokin Najeriya.