Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) za ta sake gina cibiyoyin kula da lafiya a Arewa maso Gabas
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nuna jajircewarta wajen hadin gwiwa da kungiyoyin raya kasa don sake gina cibbiyoyin kula da lafiya da aka lalata a Arewa masso Gabas. A cewar Daraktan Hukumar WHO mai kula da Afirka, Dokta Matshidiso Moeti, wanda ya yi jawabi a gaban taron ’yan jarida a Maiduguri, ranar Asabar 14 […]
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nuna jajircewarta wajen hadin gwiwa da kungiyoyin raya kasa don sake gina cibbiyoyin kula da lafiya da aka lalata a Arewa masso Gabas. A cewar Daraktan Hukumar WHO mai kula da Afirka, Dokta Matshidiso Moeti, wanda ya yi jawabi a gaban taron ’yan jarida a Maiduguri, ranar Asabar 14 ga Okttobar bana, inda aka yi nuni da cewa lokaci ya yi na na kawo dauki a jihar da sauran sassan yankin Arewa maso Gabas da kunar bakin wake ya lalata. Ta ce hukumar WHO tare da hadin gwiwar hukumomin agaji da ke aikin jinkai, sun yi aiki tukuru wajen shawo kan barkewar annoba a yankin.
Dokta Moeti, wadda ta kaddamar fafutikar kawar da cutar shan-inna da zazzzabin cizon sauro, ta ce Hukumar Lafiya ta Duniya tana tallafawa wajen bayar da magungunan zazzabin cizon sauro, cutar da ta zama jigo wajen yi wa yara kisan mummuke, kafin rikicin Arewa masso gabas ya kazance. Ta bayyana cewa hukumar ta WHO ta tattaro tawagar jami’an lafiya 113 da ta tura su Barno su taimaka wa gwamnati wajen harkokin kula da lafiya. Ta yi nuni da cewa Hadin gwiwar hukumar WHO da cibiyar kula da lafiyar kawo daukin gaugawa na Jihar Barno na da manufar shawo kan barkewar annoba da kula da lafiya cikin gaugawa. Ta yi karin haske da cewa, wannan rikicin da yake daf da karewa, inda dimbin mutanen da suka tarwatse daga al’ummominsu ke ta dawowa, akwai matukar bukatar tabbatar da gyara cibiyoyin kula da lafiya da aka lalata a amtsayin babbban yunkurin sake kafa tsarin kula da lafiya matakin farko a jihar.