Hukumar lantarki na shirin shawo kan matsalolinta – Tambuwal
Dokta Abubakar Atiku Tambuwal, wani babban jami’in hukumar bayar da wutar lantarki ta kasa, ya bayyana cewa, ’Lallai babu shakka mun gane ce wa akwai matsaloli da yawa da ya shafi bangaren Hukumar bayar da wutar Lantarki ta kasa, amma wadannan matsalolin ina ganin gwamnatin tarayya tana kokarin magancesu, domin a yanzu haka an kara […]
Dokta Abubakar Atiku Tambuwal, wani babban jami’in hukumar bayar da wutar lantarki ta kasa, ya bayyana cewa, ’Lallai babu shakka mun gane ce wa akwai matsaloli da yawa da ya shafi bangaren Hukumar bayar da wutar Lantarki ta kasa, amma wadannan matsalolin ina ganin gwamnatin tarayya tana kokarin magancesu, domin a yanzu haka an kara karfin hasken wutar lantarkin daga mega wat dubu hudu zuwa dubu biyar. Duk da cewa bai wadatar ba amma muna gani zai isa wasu wuraren.
A hirar da ya yi da Aminiya a Benin, babban birnin Jihar Edo, Dokta Abubakar Atiku Tambuwal dan Lawan Sakkwato, ya tabbatar da cewa, akwai matsala a Hukumar Bayar d aWutar Lantarki ta kasa, duk d acewa ana kokarin shawo kansu. ‘’Domin akwai matsala ta batun gas da a yanzu haka ake kan gyarawa, kuma da zarar an samu an kammala wannan gyaran, to za a sake kara karfin hasken wutar lantarkin, ta yadda za ta ishi kowa da kowa. Kuma ako ina cikin fadin kasar nan. don haka wadanda suke ce wa kamfanin wutar lantarki ba su kokari, ya kamata su yi musu adalci. Sannan su san cewa, akwai matsaloli da dama da ke tattare da wannan hukumar, wadanda idan ba kai ma’aikacin kamfanin ba ne, ba za ka sani ba,” inji shi.