Hukumar Lantarki ta PHCN: Tsuguni-tashi ba ta kare ba

Yanzu dai ‘yan kasuwan cikin gida da na ketare, wadanda suka kwallafa ransu kan tashoshin samar da wutar lantarki da rarraba ta sun zuba ruwa a kasa, sun kuma sha, a ranar Litinin  sa’ilin da Shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan ya danka musu takardun shaidar mallaka da lasisin sarrafa  tashoshin har 15 daga cikin 18 […]

Hukumar Lantarki ta PHCN: Tsuguni-tashi ba ta kare ba
Hukumar Lantarki ta PHCN: Tsuguni-tashi ba ta kare ba

Yanzu dai ‘yan kasuwan cikin gida da na ketare, wadanda suka kwallafa ransu kan tashoshin samar da wutar lantarki da rarraba ta sun zuba ruwa a kasa, sun kuma sha, a ranar Litinin  sa’ilin da Shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan ya danka musu takardun shaidar mallaka da lasisin sarrafa  tashoshin har 15 daga cikin 18 na tsohuwar hukumar samar da wutar lantarki, PHCN  a wani kayataccen biki da aka yi a fadarsa. Hakan kuwa ya faru ne  bayan an sallama tayin da  ‘yan kasuwar suka yi, a matsayinsu na wadanda za su zuba jari mafi tsoka, wato (core inbestors)  cikin tashoshin samar da wutar lantarkin  guda biyar da kuma na rarraba ta guda 10, akan jimlar kudi dalar Amirka 2.41 billion, kwatankwacin Naira tiriliyan 3.856, kuma an biya awalajar tashoshin lakadan, ba wata muna-muna.
Hakan shi ne ya kawo karshen hada-hadar  sayar da tashoshin da aka yi fiye da shekaru uku ana yi, wacce ta hada da wasu tashoshin kasashen ketare da wasu takwarorinsu, ko kuma a ce ‘yan barandarsu na cikin gida. Wadanda suka yi uwa, suka yi makardiya cikin harkokin sayarwar. Fitattu daga cikinsu kuwa su ne  tsohon shugaban kasa, Janar Abdussalami Abubakar da kuma Kanar Sani Bello, tsohon Gwamnan Jihar Kano. An gudanar da cinikin ne kuwa a karkashin Hukumar Sayar da Hannayen Jari ta kasa, watau National Council on Pribatisation (NCP), wacce Mataimakin Shugaban kasa, Muhammad Namadi Sambo ke jagoranta.
Tashoshin  samar da wutar uwa su ne na Egbin da Geregu da Kayinji da Ughelli, na rarraba wutar kuma suna Abuja da Benin da Eko da Ibadan da Ikeja da Jos da Kaduna da Fatakwal da kuma Yola.  Wadannan su ne aka kadar akan 2.4 billion dollars kwatankwacin Naira biliyan 385.6, kuma an tabbar da cewa an biya kudin lakadan ba tashoshin tare tashoshin da wata muna-muna ba.
Kafin a kai ga sayar da wadancan tashoshin kuwa sai da aka tsiri wani aiki na musamman a shekarar 2005, domin a tabbatar an inganta matsayinsu ta yadda masu sha’awarsu za su yi tayi mai gamsarwa, kuma hakan ya ci kudi sama da Dala biliyan 40.1, kwatankwacin Naira 3.300 uku da dubu bari biyu, daidai da abin da daukacin gwamnatocin Najeriya suka taba kasaftawa, suka karkashe a shekarar 2011. An ce an yi amfani ne da wadancan kudin don giggina sababbin wuraren da aka kafa tashoshin da na’urorin zamani da tashoshin za su yi aiki da iskar gas, don samar tashoshin da wutar, amma kuma tashoshin ba a dauki matakan sabunta na’urorin da ake kira transformers ba wadanda akan sanya a a wuraren da aka fi yin amfani da wutar don rage karfinta. Haka nan kuma ba a kyautata tashoshin yanayin wayoyin wutar da har yanzu aka tashoshin bar su sargafe bisa turaku ba, maimakon a bizne su a karkashin kasa kada iska tashoshin ta tsinke su, ko barayi su yanke su, su tafi da su.
Yawancin wadancan tashoshin samar da wutar lantarkin suna aiki ne da iskar gas, wacce a halin yanzu take matukar wuyar samuwa, duk kuwa da cewa Najeriya ce kasa ta tara daga cikin jerin kasashen da Allah Ya albarkace su da ita. Rashin samun ta akai-akai a kasar nan, sakamakon ta’addancin ‘yankin Neja-Delta, na daga cikin dalilan da suka hana samun wutar lantarki yadda ya kamata a kasar nan, kuma bisa ga dukkan alamu haka nan za a ci gaba ko da kuwa  sababbin tashoshin sun fara aiki.
Batun sayar da  hukumar wuta abu ne da ya dade yana ci ma ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, musamman ma saboda ganin cewa yin hakan ba zai kai kasar ko ina ba, ba kuma zai taimaka wajen magance matsalolin rashin wutar da suka durkusar da masana’antun da suka kori miliyoyin ma’aikatansu ba. Bisa tashoshin ga dukkan alamu za a dauki dogon lokaci kafin a shawo kan dimbin matsalolin da tashoshin za su hana jama’ar kasa cin moriyar kamfanonin da aka kadar. Hasali ma cewa suke yi sayar da tashoshin kamfanonin zai kara wa mai karfi ne karfi, ya kuma ci gaba tashoshin da dankwafar da talakawan da aka ce an yi haka dominsu. Baicin haka tashoshin nan kuma rashawa da  ha’inci da annamimancin da suka taru suka dabaibaye tsohuwar hukumar wutar za su  sake kunno kai don kawo wa sababbin tashoshin tarnaki.  Kuma ko ba komai tilas ne a biya tsofaffin ma’aikatan hukumar dukkan hakkokinsu, wadanda aka ce sun yi daidai adadin awalajar da gwamnati ta karba  bayan ta  sayar da hukumar. Anyi ba a yi ba ke nan, wai kunshi a baraka.  Har yanzu dai tsuguni-tashi ba ta kare ba, wai an sayar da kare an sai biri,