Hukumar NABTEB da kungiyar NATESVOSPON sun shirya taro kan ilimi
Hukumar Tsara Jarabawar Kasuwanci da Kimiyya da Fasaha ta NABTEB da Kungiyar Masu Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Najeriya (NATESVOSPON) ta shirya taron kwanaki uku kan ilimin kimiyya da fasaha da kuma koyon sana’o’in hannu. Taron wanda aka yi masa taken: “Rawar da kimiyya da fasaha za ta taka kan ilimin koyon sana’o’in hannu a […]
Hukumar Tsara Jarabawar Kasuwanci da Kimiyya da Fasaha ta NABTEB da Kungiyar Masu Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Najeriya (NATESVOSPON) ta shirya taron kwanaki uku kan ilimin kimiyya da fasaha da kuma koyon sana’o’in hannu.
Taron wanda aka yi masa taken: “Rawar da kimiyya da fasaha za ta taka kan ilimin koyon sana’o’in hannu a ci gaban Najeriya” an kaddamar da shi ne a Abuja, jiya.
Da take jawabi, Shugabar Hukumar Tsara Jarabawar Kasuwanci da Kimiyya da Fasaha ta NABTEB, Farfesa Ifeoma M. Isiugo-Abanihe ta yaba wa kungiyar NATESVOSPON da ta shirya taron.
Ta bayyana cewa taron ya nuna irin namijin kokarin da kungiyar take yi na ganin hukumar NABTEB ta samu nasara kan yada ilimin koyon sana’o’in hannu da take yi a Najeriya
Da yake jawabi, Karamin Ministan Ilimi, Farfesa Anthony Anwuka wanda Mai Taimaka Masa Ta Fuskar Siyasa, Frank Ibezim ya wakilta, ya jaddada alfanun ilimin kimiyya da fasaha da kuma na koyon sana’o’in hannu.
Ya ce babu kasar da za ta cigaba ba tare da baiwa ilimin koyon sana’o’i muhimmanci ba.
Ya bayar da misali ga kasashen da suka cigaba kamar Amurka da China da Rasha da sauransu in da ya ce muhimmancin da suka baiwa ilimin kimiyya da fasaha da koyon sana’o’in hannu shi ya kai su ga matsayin da suke a yanzu.