Hukumar NAHCON ta kai dauki ga alhazan jirgin yawo 6000
Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ta magance aukuwar wani babban abin kunya da ka iya bata sunan kasar nan, inda ta yi kokarin kwashe alhazan jirgin yawo sama da dubu shida da aka yi watsi da su zuwa kasa Mai tsarki. Alhazan wadanda mafi yawansu sun sayi tikitin jirgin sama ne daga kamfanonin jiragen, […]
Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ta magance aukuwar wani babban abin kunya da ka iya bata sunan kasar nan, inda ta yi kokarin kwashe alhazan jirgin yawo sama da dubu shida da aka yi watsi da su zuwa kasa Mai tsarki.
Alhazan wadanda mafi yawansu sun sayi tikitin jirgin sama ne daga kamfanonin jiragen, ba su samu tashi ba ne saboda rashin izinin shiga Saudiyya daga ofishin Jakadancin Saudiyya a Najeriya, inda aka bar su da tunani kan makomarsu kafin Hukumar NAHCON ta kai musu dauki.
Hukumar ta yi amfani da damar diflomasiyya da kyakkyawar dangantakar kasuwanci da ke tsakanin Saudiyya da kamfanin jiragin sama na -Flynas- don jigilar alhazan saboda jiragen sama da dama sun sauka a kasa Mai tsarki.
Da yake mika godiyar mambobinsa ga hukumar Shugaban kungiyar Masu Jigilar Mahajjata da ’Yan Umara ta Najeriya (AHUON), alhaji Abdulfattah Abdulmajeed ya yaba wa hukumar kan irin taimakon da ta yi wa ’ya’yan kungiyarsa, inda ta kai musu dauki, ya ce ba somin sanya hannun hukumar ba, da wakilan kungiyar da dama sun talauce kuma an kama su.
Ya yi alkawarin ci gaba bayar da hadin kai da goyon bayan kungiyarsa wajen tabbatar da inganta yadda ake gudanar aikin hajji da kuma jin dadin alhazan Najeriya, inda ya yi kira ga hukumar da koyaushe ta rika sanya kungiyarsu a al’amuran da suka shafi harkokin Hajji a Najeriya.