Hukumar NCC a shirye take wajen biyan bukatun masu tu’ammali da kayan sadarwa – danbatta
Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Najeriya (NCC) a shirye take wajen kare hakki, saurare da magance koke-koke da matsalolin masu tu’ammali da kayan sadarwa a Najeriya. Haka kuma a shirye hukumar take wajen ba da kariya daga masu neman ha’intar al’umma ta wannan fanni. Babban Mataimakin Shugaban hukumar, Farfesa Umar Garba danbatta ne ya […]
Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Najeriya (NCC) a shirye take wajen kare hakki, saurare da magance koke-koke da matsalolin masu tu’ammali da kayan sadarwa a Najeriya. Haka kuma a shirye hukumar take wajen ba da kariya daga masu neman ha’intar al’umma ta wannan fanni. Babban Mataimakin Shugaban hukumar, Farfesa Umar Garba danbatta ne ya bayyana haka.
Farfesa danbatta ya bayyana haka ne a a kwanakin baya, yayin gudanar da wani taron da aka shirya wa masu tu’ammali da kayan sadarwa a garin Numan, Jihar Adamawa. Ya ce babban makasudin taron, an shirya shi ne domin fadakar da al’umma, yadda za su kauce wa sayen kayan sadarwa marasa inganci, da kuma kare kansa daga maha’inta da ke cutar da mutane ta wannan fanni.
Ya ce wannan tsari da hukumar ta dauka, na rangadi da tarukan fadakar da al’umma, shi ne tsari mafi dacewa, mai rahusa wajen kare al’umma daga asara da kare su daga macuta.
Kamar yadda ya ce: “Domin ganin an fadakar da masu tu’ammali da kayayyakin sadarwa kuma an kare su daga kowace irin zamba, hukumar NCC ta fito da tsare-tsare daban-daban domin ganin cewa sun fadaka, sun iya yin zabin kayan da suka dace domin cin gajiyar kudinsu.
“Wadannan tsare-tsare sun hada da:
1-Shirya tarukan fadakarwa a garuruwa daban-daban a fadin kasar nan.
2-Rarraba takardun bayanan fadakarwa da ilimantarwa ga al’umma.
3-Fadakarwa da fayyace muhimman bayanan da za su amfani masu tu’ammali da kayan sadarwa ta hanyar yanar gizo da kafafen zumunta na zamani kamar Facebook, Twitter da sauransu.
4-Amsa tambayoyin al’umma ga wadanda suka kira lambar hukumar NCC da aka tanada domin wannan bukata, kiran kyauta ne, wato lambar 622.
5-Shiga gidajen rediyo domin gabatar da shirye-shiryen fadakar da al’umma wajen sanin hakkokinsu da suka danganci tu’ammali da kayan sadarwa.”
Ya ce tsarin mulkin kasar nan ya tanadar da ’yanci da hakkoki daban-daban ga al’ummar kasa, wadanda suka wajaba a tabbatar da an ba kowane dan kasa su.
Farfesa danbatta ya kara da cewa: “Haka kuma, Hukumar NCC, a matsayinta na hukumar da ke da alhakin kula da daidatuwar al’amuran da suka danganci sadarwa da dangoginsu da kuma kare masu tu’ammali da kayan sadarwa daga maha’inta tana kula da dukkan yadda al’amura a sashin ke gudana, domin tabbatar da cewa ba a cuci wani ko an ha’ince shi ta fuskar tu’ammali da kayan sadarwa ba a kasar nan; musamman wajen ilimantar da su da fadakar da su yadda ya kamata.
“Wadannan hakkoki sun hada da sanar da mutum cikakken bayani kan tsarin da ya saya. Bayyana masa cikakken bayani da harshen da zai iya fahimta. Wadannan bayanai ne za su kasance jagora ga mutum, domin sanin abin da ya bukata, ya sanya kudinsa ya saya, ko ya biya.”
Shugaban na NCC ya ce don haka ya zama wajibi ga kamfanonin waya su rika yin magana da abokan huldarsu, suna bayyana masu ayyukansu cikin harsunan da suke fahimta kuma da bayani mai gamsarwa da fahimtarwa. Lallai ne bayani ya zama mai gamsarwa, na gaskiya kuma a kan lokaci. Irin wadannan bayanai, su za su taimaki al’umma masu tu’ammali da kamfanonin sadarwa domin sanin irin tsare-tsarensu.
“A Hukumar NCC, muna daraja abokan huldar kayan sadarwa ta hanyar hidimominmu zuwa gare su, domin su samu gamsarwa a dukkan abin da suka saya da kudinsu, wanda ya shafi kayan sadarwa. Haka kuma, idan sun shiga matasala da wani kamfanin sadarwa, hukumar tana yin tsayin daka wajen ganin ta kwato masu hakkokinsu. Haka kuma tana nan tana gadi, domin kare al’umma daga duk wata cutarwa.
“An zabi tsarin ilimantar da masu tu’ammali da kayan sadarwa ne domin ba su kariya daga duk masu neman cutar da su ko ha’intarsu ta fuskar mu’amala. Tsari ne mai rahusa kuma mai biyan bukata wajen hidimta wa al’umma da ke tu’ammali da kayan sadarwa.”