Hukumar NCC: Mai saye sarki ne a fadar kasuwa
Hukumar NCC ta gudanar da gagarumin taron fadakarwa da ilimantarwa ga al’umma masu tu’ammali da kayan sadarwa, karo na 30 a garin Numan Jihar Adamawa. Taron ya hada mutane da yawa, inda aka gudanar da shi cikin tsari da gamsarwa. Ya ce wannan tsari da hukumar ta dauka, na rangadi da tarukan fadakar da al’umma, […]
Hukumar NCC ta gudanar da gagarumin taron fadakarwa da ilimantarwa ga al’umma masu tu’ammali da kayan sadarwa, karo na 30 a garin Numan Jihar Adamawa. Taron ya hada mutane da yawa, inda aka gudanar da shi cikin tsari da gamsarwa.
Ya ce wannan tsari da hukumar ta dauka, na rangadi da tarukan fadakar da al’umma, shi ne tsari mafi dacewa, mai rahusa wajen kare al’umma daga asara da kare su daga macuta. Shirin ya hada al’umma da kuma jami’an kamfanonin sadarwa daban-daban, inda aka yi musharaka, aka tattauna al’umura daban-daban da suka danganci mu’amala tsakanin sassan biyu, wato tsakanin kamfanonin sadarwa da kuma masu tu’ammali da su, ta wajen sayen kayayyakinsu.
Da yake jawabinsa na bude taron, Daraktan Al’amuran Abokan Huldar Sadarwa na hukumar NCC, Mista Abdullahi Maikano, wanda Mataimakinsa, Alhaji Isma’ila Adedigba ya wakilta, ya ce: “A hukumar NCC, babban burinmu shi ne biyan bukatun abokan huldar masu tu’ammali da kayan sadarwa. A wurinmu, mutane masu saye, sarakuna ne a kasuwar kayan sadarwa. Duk wani aiki ko wata dawainiya da za mu yi, ko muke yi, muna yi domin dadad wa al’umma da kare su daga maha’inta, domin ganin sun ci gajiyar dukkan wani tsarin kayan sadarwa da suka fansa ko kuma suka saya.”
Taken taron na bana shi ne, Bayani Da Fadakarwa Su Ne Tsanin Abokan Hulda. Idan za a iya tunawa, a watan Maris da ya gabata, Hukumar NCC ta bayyana 2017 a matsayin shekarar kula da abokan hulda, don haka abokan hulda suna da hakkin a saurare su, a fadakar da su, a ba su kariya daga kowace irin cutarwa a yayin tu’ammalinsu da kayan sadarwa. Don haka wannan tsari abu ne mai kyau, da zai ba mutane damar bayyana dukkan korafe-korafensu.
Ga duk mai korafi ko tambaya dangane da al’amuran da suka shafi kayayyaki ko tsare-tsaren kamfanonin sadarwa, mutum zai buga layin NCC mai lamba 622 kyauta, domin bayyana kokensa ko gabatar da tambayarsa. Idan kuma mutum na son ya dakatar da sakonnin da ake aiko masa ba da son ransa ba, zai iya amfani da lambar 2442 domin aika tes, da nufin a dakatar da turo masa irin wadannan sakonni da ba ya bukata.
Haka kuma, ga masu amfani da shafin Twitter, mutum zai iya aika sako ta adireshin: @consumersncc ko kuma ta hanyar adireshin turakar hukumar na yanar gizo (web portal): www.consumer.ncc.gob.ng <http://www.consumer.ncc.gob.ng>
Muna fata za a yi amfani da wadannan tsare-tsare domin cin gajiyarsu.