Hukumar NCC ta bai abokan hulda tabbacin kare hakkinsu

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ba wa abokan hulda tabbacin ci gaba da tabbatar da suna cin moriyar kudin da suka kashe. Hukumar ta ce za ta ci gaba da magance kalubalen da ke fuskantar masana’antar sadarwa. Shugaban Hukumar NCC,  Farfesa Umar Dambatta, wanda ya yi jawabi a ranar bikin Hukumar NCC da ya […]

Hukumar NCC ta bai abokan hulda tabbacin kare hakkinsu
Hukumar NCC ta bai abokan hulda tabbacin kare hakkinsu

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ba wa abokan hulda tabbacin ci gaba da tabbatar da suna cin moriyar kudin da suka kashe. Hukumar ta ce za ta ci gaba da magance kalubalen da ke fuskantar masana’antar sadarwa.

Shugaban Hukumar NCC,  Farfesa Umar Dambatta, wanda ya yi jawabi a ranar bikin Hukumar NCC da ya gudana a dakin taro na Tafawa Balewa a Kasuwar Baje Koli ta Kasa da Kasa  da ke Legas a kwanakin baya, ya ce a matsayin hukumar na mai sanya ido tana sane da dimbin nauyin da ke kanta na kare bukatun masu ruwa-da- tsaki.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Mataimakin Darakta Mai Kula da Harkokin Abokan Hulda, Mista Ismail Adedigba, ya ce an shirya taron ne domin samun tabbacin  hanyar  warware matsalolin da kamfanonin sadarwa da suke fuskanta.

Ya ce Hukumar NCC a matsayinta ta mai sanya ido kan harkokin sadarwa yana daga cikin al’amuranta  na yau da kullun cewa ba za a samu nasara ba, ba tare da abokan hulda ba,  sakamakon sanin muhimmanci abokan hulda a kamfanonin sadarwa. “Wannan shi ne shaida na tsarin ajandojinmu takwas na hukumar domin tallafawa da kiyaye hakkin abokan hulda da samar da bayanai da ilimi domin zabin amfani da kamfanonin sadarwa da karfafa su,” inji shi.

Ya ce  Hukumar NCC a matsayinta ta mai tsarin gunadanarwa ta kamfanonin sadarwa ta tsara yanayin ajiye korafi na lokacin da abokin hulda ya kai kan kamfanin da yake amfani da shi.

Kuma hukumar ta tanadi hukunci don hukunta wanda aka samu da laifi.

Ya ce daga cikin abubuwan da suke damun abokan hulda da hukumar take kokarin samar da mafita akwai tura sakon kasuwanci da aka fi sani da sakon da ba ka bukata ba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos