Hukumar NCC ta gudanar da taron ganawa da masu amfani da tarho karo na 90 a Abiya
A wani bangare na abin da Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ke gudanarwa na ganawa da masu amfani da tarho ta hanyar bayar da bayanai da ilimantarwa, hukumar ta gudanar da taro na 90 na isa ga masu amfani da tarho (COP) mai taken BAYANI DA ILIMANTARWA A MATSAYIN GINSHIkAN KARE MASU AMFANI DA TARHO. […]
A wani bangare na abin da Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ke gudanarwa na ganawa da masu amfani da tarho ta hanyar bayar da bayanai da ilimantarwa, hukumar ta gudanar da taro na 90 na isa ga masu amfani da tarho (COP) mai taken BAYANI DA ILIMANTARWA A MATSAYIN GINSHIkAN KARE MASU AMFANI DA TARHO.
An shaida wa mahalarta taron cewa an tsara shirin ne domin a sanya masu amfani da tarho su bayyana damuwarsu ko fahimtarsu kan ayyukan kamfanonin tarho tare da jin ra’ayinsu domin bayar da tasu gudunamwar ga hukumar wajen tsara yadda za a inganta ayyukan tarho.
Mataimakin Daraktan Harkokin Masu Amfani da Tarho na Hukumar NCC, Ismail Adedigba wanda ya wakilci Daraktan Harkokin Masu Amfani da Tarho na Hukumar, Abdullahi Maikano, a wajen taron ya nanata yunkurin hukumar da dabarun da ta bullo da su domin magance matsalolin da masu amfani da tarho suke fuskanta, kamar kiran layi na “622” a kyauta da aka ajiye gare su don isar da kuka kan matsalolin da aka kasa warwarewa ga kamfanonin tarho da suke hulda da su. Adedigba ya kuma sanar da mahalartan kan takaitacciyar hanyar “Kada-A-Dame (DND) ta “2442” da ke ba masu amfan da tarho magance karbar sakonnin da ba su bukata.
Kuma ya yi magana kan sauran tsare-tsaren hukumar kamar Majalisar Masu Amfani da Tarho (TCP) wadda kafa ce ta musayar ra’ayi a tsakanin masu amfani da tarho da kamfanonin tarho da aka tsara domin samar da maslaha kan matsalolin da suke tasowa. Game da zargin cewa akwai wata iskar guba da ake samu daga turakun isar da sakonnin sadarwa, Adedigba ya ce babu wata shaida da tabbatar da wannan zargi na cewa turakun aikewa da sakonnin da suke karba suna cutarwa ga lafiya dan Adam.
Taron ya samu halartar wakilai daga sassa daban-daban na Hukumar NCC da kamfanonin tarho da Kwamishinan Kimiyya da kere-kere na Jihar Abiya Cif Fabian Nwankwo da jami’an Hukumar NSCDC da mutanen karamar Hukumar Osisioma Ngwa da ’yan jarida da masu amfani da tarho da kuma wakilai daga kungiyoyi masu zaman kansu, kuma an bayar da shawarwari masu ma’ana don bunkasa harkokin sadarwa da abubuwan da suke shafarsu da kuma masana’antar.