Hukumar NCC ta sabunta lasisin MTN

A ranar Talatar da ta gabata ne aka ruwaito cewa Hukumar da ke Kula da Kamfanonin Sadarwa wato (NCC) ta sabunta lasisin kamfanin sadarwa na MTN kan kudi Dala miliyan 94. An dai bai wa kamfanin lasisin farko ne a shekarar 2001 wanda kuma zai kare a watan Fabrairun badi. Amma a yanzu bayan sabunta […]

Hukumar NCC ta sabunta lasisin MTN
Hukumar NCC ta sabunta lasisin MTN

A ranar Talatar da ta gabata ne aka ruwaito cewa Hukumar da ke Kula da Kamfanonin Sadarwa wato (NCC) ta sabunta lasisin kamfanin sadarwa na MTN kan kudi Dala miliyan 94.

An dai bai wa kamfanin lasisin farko ne a shekarar 2001 wanda kuma zai kare a watan Fabrairun badi. Amma a yanzu bayan sabunta shi zai kare ne a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2021 wato kimanin shekaru shida ke nan.
Hakazalika, darajar hannun jarin kamfanin MTN ya fadi da kaso 25 cikin 100 bayan Hukumar da ke Kula da Kamfanin Sadarwa wato (NCC) ta ci tarar kamfanin naira triliyan daya da biliyan 400.
Kodayake, kamfanin MTN na kokarin sasantawa da hukumomi kan tararar da aka ci shi saboda gazawarsa wajen toshe layukan wadanda ba su kammala rijistar su ba, inda hukumar ta bukaci kamfanin ya biya tarar zuwa ranar Litinin 16 ga watan nan.
Hakazalika, Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce ba ya wata tattauanawa da kamfanin bisa tarar. Ya ce kamata ya yi MTN ya tattauna da Hukumar NCC, amma ba bangaren zartarwa ba.
A lokacin da Farfesa Osinbajo ya bayyana kadarorinsa, ya ce ya mallaki hannun jarin kamfanin MTN.
A ranar Litinin da ta gabata ne kamfanin ya bayyana cewa ya fara tattaunawa don neman sassauci bayan ya turo wata tawaga daga Afirka ta Kudu zuwa Abuja. Har ila yau, wani jami’i a Hukumar NCC ya ce sun fara tattaunawa da tawagar, sai dai tabbatar da cewa yanzu batun yana hannun Ofishin Mai Bai wa Shugaban kasa Shawara, ba hukumar ba.
Najeriya ita ce babbar kasuwar kamfanin, inda yake da layuka fiye da miliyan 62 wadanda jama’a suke amfani da su, kamar yadda bayanai daga Hukumar NCC suka bayyana.

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba

Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano

Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun

Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki