Hukumar NCC ta sha alwashin gamsar da ’yan Najeriya
Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) da Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Najeriya (NCC) sun yi hadin gwiwa domin magance matsalolin da ake samu dangane da al’amuran sadarwa a birni da kewaye. Mataimakin Shugaban hukumar, Farfesa Umar danbatta ne ya bayyana haka, a lokacin da ya kai wa Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Muhammad […]
Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) da Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Najeriya (NCC) sun yi hadin gwiwa domin magance matsalolin da ake samu dangane da al’amuran sadarwa a birni da kewaye.
Mataimakin Shugaban hukumar, Farfesa Umar danbatta ne ya bayyana haka, a lokacin da ya kai wa Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Muhammad Musa Bello ziyara a ofishinsa, Abuja.
“La’akari da matsayin Abuja a yau, ya dace a ce tana da ingantattun hanyoyin sadarwa, sai dai ba haka abin yake ba har zuwa yau. Wannan ya tabbatar mana da hakikanin yanayi, cewa Abuja tana fuskantar wasu kalubale da ke kawo cikas wajen tabbatar da juyin-juya-hali a harkar sadarwa nan gaba. Babban Birnin Tarayya na da matsaloli mafiya wuyar sha’ani, wajen samun ingantattun hanyoyin sadarwa, idan aka kwatanta shi da sauran birane a fadin kasar nan, saboda wasu dalilai da nan gaba za mu kara haske a kansu,” kamar yadda shugaban na NCC ya shaida wa Ministan Babban Birnin Tarayya.
Ya zayyana wasu daga cikin matsalolin da suka hada da girke tashoshin sadarwa a Abuja, kudin haraji da Babban Birnin Abuja ke amsa daga kamfanonin sadarwa tun a 2006, dokokin da suka shafi harkokin sadarwa kan al’amuran da suka faru a Abuja, matsalolin gine-ginen hanyoyi a Abuja, jinkirin da ake samu wajen bayar da izinin kafa tashoshin sadarwa ko canja masu matsuguni da kuma dabbaka kudurorin da Majalisar Zartarwa ta kasa ta gindaya dangane da ninkin kudin haraji ko tara da ake amsa game da kayayyakin kamfanonin sadarwa. Game da batun girke tashar sadarwa, Shugaban NCC ya ce kamfanonin a shirye suke su girke tashoshin nasu amma “har yanzu ba mu samu bayanin ka’idojin yin haka ba daga hukumar Babban Birnin Tarayya.”
Ya kara da cewa: “Muna rokon Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta amince da ka’idojin hukumar NCC dangane da kafa tashar kamfanin sadarwa. Haka kuma, wuraren da aka ware domin kafa tashoshin sadarwa sun yi kadan kuma ba su dace da tsarin da kamfanonin ke bukata ba. Ya dace a ce ana musharaka da kamfanonin sadarwa, kafin a ware masu wuraren da ake tanadar masu, domin kafa tashoshinsu, domin su dace da samun netwok da kuma yanayin da ya dace da masu kafa tashar rediyo. Haka kuma, idan har an lura da cewa wuraren ba za su iya daukar tashar sadarwa ba, to hukumar FCT ta amince wa kamfanonin su ci gajiyar kashin kansu.