Hukumar NDE ta fara koya wa matasa 1,320 sana’o’i
Hukumar Samar da Aikin yi ta Kasa (NDE)a Jihar Kano ta fara horar da matasa 1,320 kan sana’o’i daban-daban a karkashin shirin hukumar na B-NOAS. Matasan maza da mata suna koyon sana’o’in da suka hada da kayan kwalliya da aikin kafinta da walda da dinki da girke-girke da sarrafa na’urar kwanfuta da sauransu. Da yake […]
Hukumar Samar da Aikin yi ta Kasa (NDE)a Jihar Kano ta fara horar da matasa 1,320 kan sana’o’i daban-daban a karkashin shirin hukumar na B-NOAS.
Matasan maza da mata suna koyon sana’o’in da suka hada da kayan kwalliya da aikin kafinta da walda da dinki da girke-girke da sarrafa na’urar kwanfuta da sauransu.
Da yake jawabi a wajen taron, Darakta Janar na Hukumar, Dokta Nasiru Ladan, ya ce shirin an tsara shi da nufin tallafa wa dimbin matasa marasa aikin yi a fadin jihar don su dogara da kansu.
Alhaji Ladan wanda Malam Umar Yusuf ya wakilta ya ce an kafa hukumar ce da nufin kakkabe talauci ta hanyar samar da aikin yi ga matasan da ba su da aikin yi a kasar nan.
Ya ce sana’ar hannu ita ce hanyar dorewar kowace kasa da ke da marasa aikin yi a cikinta, inda ya yi kira ga wadanda suka amfana su yi amfani da damar da suka samu wajen dogaro da kansu tare da sama wa wadansu abin yi.
A jawabin maraba, Shugaban Hukumar a Jihar Kano Alhaji Ahmed Iliyasu, ya ce shirin horarwar hanya ce da za ta bunkasa arzikin matasan, inda ya nemi matasan su saka wa kokarin gwamnati ta hanyar mayar da hankali a kan sana’o’in da za su koya tare da sarrafa abin da za su koya don su zama masu dogaro da kawunansu.
Shugaban Hukumar ya ce matasan da za su koyi sana’o’in an debo su ne daga dukkan kananan hukumomi 44 da ke jihar a kokarin hukumar na ganin an kara fadada shirin zuwa karkara.
Alhaji Iliyasu ya kara da cewa horarwar za ta kai tsawon wata shida inda a karshe hukumar za ta tallafa musu da dan abin da za su fara sana’a da shi.
Da suke jawabi wadansu daga cikin wandanda za a koyar, Jamila Jibril Sa’id da Muktar Garba Sani sun yaba wa Gwamnatin Tarayya da Hukumar NDE game da kirkiro da shirin, a cewarsu ko shakka babu zai taimaka wajen rage yawan dogaron da matasa ke yi kan gwamnati don ta sama musu ayyukan yi.