Hukumar NDE ta koya wa mata da matasa 700 sana’o’i a Katsina

A kokarin rage zaman kashe wando da samar wa matasa aikin yi, Hukumar Samar da Aikin Yi ta Kasa (NDE) ta horar da mata da matasa 700 sana’o’in hannu daban-daban a Jihar Katsina. Da yake jawabi a wajen taron ba su bashin kudi don ci gaba da  sana’o’in da suka koya, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu […]

Hukumar NDE ta koya wa mata da matasa 700 sana’o’i a Katsina

Wakilin Gwamnan Katsina yana miqa wa wata da ta ci gajiyar kuxin tallafin

A kokarin rage zaman kashe wando da samar wa matasa aikin yi, Hukumar Samar da Aikin Yi ta Kasa (NDE) ta horar da mata da matasa 700 sana’o’in hannu daban-daban a Jihar Katsina.

Da yake jawabi a wajen taron ba su bashin kudi don ci gaba da  sana’o’in da suka koya, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, wanda Kwamishinan Gidaje da Yawon Bude-Ido na Jihar Alhaji Abubakar Yusuf ya wakilta, ya ce wannan aiki da Hukumar NDE take yi na samar wa matasa aiki, ya zo a daidai da niyyar Gwamnan Jihar na samar wa al’umma ayyukan yi don su dogara da kansu.

Waxansu daga cikin waxanda suka ci moriyar shirin

Gwamnan ya ce a kwanakin baya Hukumar NDE ta raba wa  mata da matasa a garin Daura Naira miliyan 20 yanzu kuma ta sake dawowa Katsina ta raba Naira miliyan bakwai, inda ya bayyana hakan da cewa ba karamin ci gaba ba ne.

Sai ya yi kira ga wadanda aka koya wa sana’o’in cewa su rike abin da suka koya da mutunci domin zai iya zama sanadin arzikinsu don ba a raina sana’a ko jari.

A nata jawabin, Kwamishinar Harkokin Mata, Dokta Badiyya Hassan Mashi, cewa ta yi a baya bayan nan Gwamna Aminu Masari, ya ba da Naira miliyan 40 aka raba wa mata 400 kyauta don su samu sana’ar da za su dogara da kansu.

Dokta Badiyya Mashi, ta kara da cewa irin wadannan sana’o’i da tallafi da ake bai wa mata yana rage zaman kashe wando a tsakanin al’umma domin mata su ne rabin al’umma.

Sannan ta ce nan gaba Gwamnatin Aminu Masari za ta bullo da wani tallafi da za a bai wa mata 200 masu marayu don kula da su.

A jawabin, Babban Daraktan Hukumar NDE ta Kasa Dokta Nasir Muhammad Ladan, cewa ya yi wadannan sana’o’i da tallafi da ake bai wa mata da matasa da ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a yi ne don rage zaman kashe wando, kuma shi ne yanzu ake yi.

Dokta Nasir Ladan, ya ce nan gaba akwai wani shiri da Hukumar NDE da za shirya taren da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) domin bai wa wadanda aka horar sana’o’in rance har na Naira niliyan 750.

Wadansu daga cikin matasan da suka ci gajiyar shirin da suka zanta da Aminiya sun ce sun gama makaranta amma rashin aikin yi ya sa suka shiga shirin don zai taimaka musu ya rage musu zaman kashe wando. Sun ce wadansunsu sun koyi aski wadansu hada man shafawa wadansu sabulu, kuma Hukumar NDE ta ce idan suka yi abin sayarwar ita za ta saya.