Hukumar NDIC  ta nemi masu ajiya a banki su kai mata karar duk bankin da ya cuce su

Hukumar  Bada Kariya ga Masu Ajiya a Bankuna (NDIC) ta  bukaci masu hulda da bankuna a kasar nan su gaggauta sanar da ita kan duk wata cuta ko almundahana da wani banki ya yi musu don daukar matakin da ya dace. Shugaban Hukumar NDIC, Alhaji Umar Ibrahim ya bayyana  haka lokacin bikin bajekoli karo na […]

Hukumar NDIC  ta nemi masu ajiya a banki su kai mata karar duk bankin da ya cuce su

Hukumar  Bada Kariya ga Masu Ajiya a Bankuna (NDIC) ta  bukaci masu hulda da bankuna a kasar nan su gaggauta sanar da ita kan duk wata cuta ko almundahana da wani banki ya yi musu don daukar matakin da ya dace.

Shugaban Hukumar NDIC, Alhaji Umar Ibrahim ya bayyana  haka lokacin bikin bajekoli karo na 40 da Cibiyar  ’Yan Kasuwa da Masana’antu da Ma’adinai da Aikin Gona ta Jihar Kano(KACCIMA) ta shirya.

Alhaji Umar Ibrahim wanda Shugaban Shiyya na Hukumar da ke Kano Alhaji Bashir Alhassan ya wakilta, ya yi kira ga jama’a su guji ajiyar kudi a gidaje ko shaguna don guje wa hadarin gobara ko sata ko  fashi da makami. “Idan bankin da yake da inshora ya karye hukumar za ta mayar wa masu ajiya a manyan bankunan kasuwanci  kudadensu akalla Naira dubu 500 Haka wadanda ke amfani da kananan bankunan kasuwanci za su samu kimanin  Naira dubu 200,” inji shi.

Ya ce a koyaushe hukumarsu tana kokarin bullo da sababbin tsare-tsare don ganin ta kara samun amincewa daga jama’a dangane da ajiyarsu a bankuna .

Shugaban ya ce Hukumar NDIC tana hada kai da Kungiyar KACCIMA don yin amfani da bikin na bajekoli domin kara wayar da kan al’umma game da ayyukan hukumar.

A jawabin Mataimakin Shugaban Kungiyar KACCIMA Ambasada Usman Hassan Darma, ya yaba wa kokarin Hukumar NDIC game da gudunmawar da take bayarwa na habakar tattalin arzikin kasa ta hanyar  kula tare da bayar da kariya ga kudaden al’umma a bankuna wanda a  cewarsa ya janyo al’umma suka samu natsuwa da yin amfani da banki a kasar nan.