Hukumar NDLEA ta cafke masu fiton kaya

Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA)  ta kame wasu mutane da ke fiton kayayyaki a tashar jirgin saman na kasa-da-kasa da ke Legas da miyagun kwayoyi. Cikin kayan har da tabar wiwi da kuma hodar ‘mefitamin’, wanda nauyinsu ya kai kilogiram 55.6. An boye su cikin kayan abinci da kuma gashin da […]

Hukumar NDLEA ta cafke masu fiton kaya
Hukumar NDLEA ta cafke masu fiton kaya

Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA)  ta kame wasu mutane da ke fiton kayayyaki a tashar jirgin saman na kasa-da-kasa da ke Legas da miyagun kwayoyi.
Cikin kayan har da tabar wiwi da kuma hodar ‘mefitamin’, wanda nauyinsu ya kai kilogiram 55.6. An boye su cikin kayan abinci da kuma gashin da mata ke amfani da shi wajen kitso. An cafke wannan mummunar  hajar  ce  a lokacin da suke  kokarin shiga  jirgi zuwa kasar Sin da kuma Afirka ta Kudu.
Da yake wa  taron manema  labarai  jawabi,  shugaban hukumar,  mai  kula da  tashar jirgin saman  Murtala Mohammed, Malam Hamza  Umar  ya ce wannan kamun shi ne  irinsa na  farko  da ya fi yawan adadin kayan tun farkon wannan shekarar.
daya daga  cikin wadanda  aka  kama,  wanda  dan asalin Jihar Anambra  ne, dan kasuwa mazaunin kasar Guinea, mai suna Sylbester Nmadi Augustine, amma da  fasfon kasar Guinea  da ke da sunan Keita Mamady ya ce  an umurce  shi ne da ya kai kwayar Hong Kong kana ya wuce Guangzhou, inda  za a biya shi ladar wannan aikin nasa.  
Mutun na biyu mai suna Samuel Williams ya shaida wa manema labarai cewa abokinsa ne da ke  zaune a Afirka Ta Kudu ya nemi ya  sawo masa gashin mata da ake karawa wajen kitso. “Da aka kawo, sai na ba masu aikewa da kaya kasar waje, ashe wadanda suka kawo gashin sun boye miyagun kwayoyi ciki, ni ban sani ba”, inji shi.
Mutumi na 3, dan asalin Jihar Ogun, mai suna Adams Adewumi ya ce abokin aikinsa ne Samuel ya ba shi sundukin don ya kai masa  cikin jirgi mai tafiya kasar Afirka ta Kudu, amma bai fadda masa akwai wannan mugunyar hajar ba, sai da jami’an hukumar ta NDLE suka gano ashe an boye ta a ciki, kuma shi Samuel bai musanta shi ya aike shi ba.
Shugaban hukumar  ya ce da zaran sun kammala  bincike za su gurfanar da wadanda ake tuhumar a kotu.