Hukumar NDLEA ta gano wuraren sarrafa miyagun kwayoyi

Rundunar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta ce, a shekara ta 2011 ne ta gano dakin gwaje-gwajen farko da ake hada miyagun kwayoyi a boye, domin sarrafa su zuwa nau’i daban-daban cikin kasar nan. Daga wancan lokaci zuwa yanzu an gano irin wadannan dakunan gwajin miyagun kwayoyi guda shida a Legas da […]

Hukumar NDLEA ta gano wuraren sarrafa miyagun kwayoyi
Hukumar NDLEA ta gano wuraren sarrafa miyagun kwayoyi

Rundunar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta ce, a shekara ta 2011 ne ta gano dakin gwaje-gwajen farko da ake hada miyagun kwayoyi a boye, domin sarrafa su zuwa nau’i daban-daban cikin kasar nan. Daga wancan lokaci zuwa yanzu an gano irin wadannan dakunan gwajin miyagun kwayoyi guda shida a Legas da guda daya a Jihar Anambra, tare da gonakin noman tabar wiwi barkatai, wanda tuni hukumar ta rufe su tare da share filayen gonakin.
Shugaban Hukumar NDLEA ta kasa, Alhaji Ahmadu Giade, shi ne ya fadi haka a ranar Alhamis ta makon jiya a Ibadan a wajen gangamin jami’an tsaro da suka cinna wuta domin lalata miyagun kwayoyo da hukumar ta kama a sassa daban daban na Jihar Oyo.
“A daidai wannan lokaci na karshen shekara da shirin zaben badi, Hukumar NDLEA ta kammala daukar tsauraran matakan tsaro a dukkan kan iyakokin Najeriya da kasashe makwbta tare da ci gaba da kyautata dangantakar hadin gwiwa a tsakaninta da takwarorinta na ciki da kasashen duniya.” inji Ahmadu Giade, wanda ya ci gaba da cewa, “ina tabbatar maku cewa, babu sauran wata kafa ta hada-hadar miyagun kwayoyi a cikin kasar nan. Su ma hamshakan mutane masu aikata irin wannan danyen aiki wannan ita ce ranar bakin ciki gare su.”
Cikin jawabinta, Kwamandar rundunar NDLEA ta Jihar Oyo, Uwargida Omolade Faboyede, cewa ta yi “yau a Jihar Oyo mun kama miyagun kwayoyi masu nauyin fiye da kilogiram dubu 20 da aka kiyasta kudinsu a kan Naira miliyan 65 da za a lalata su tare da kona su kurmus. Miyagun kwayoyin sun hada da ganyen tabar wiwi da koken da heroyin da makamantansu.”
Uwargida Faboyede ta mika godiya ga Gwamnan Jihar Oyo a kan umarnin da ya ba ma’aikatar lafiya da ta tabbatar da gina cibiyar nazarin magungun da bullo da matakan rage yawan bullar magungunan bogi da daidaita matsayinsu.
Da yake zantawa da wakilinmu Mataimakin Kwamandan rundunar ta NDLEA a Jihar Oyo, Alhaji Isa Ibrahim Yusuf, cewa ya yi “abu na farko da ya kaimu ga samun nasarar kama miyagun kwayoyi masu yawa fiye da na bara shi ne, irin zage damtse da muka yi da mayar da hankali wajen neman bayanai a kan irin wadannan miyagun mutane.
Abu na biyu kuma shi ne kyakkyawan hadin kai a tsakaninmu da rundunonin tsaro na sojan kasa da sama  da ‘yan sanda da kwastam da SSS da NSCDC da makamantasu da muke gudanar da aikin hadin guiwa domin ceto miliyoyin matasa daga fadawa halin ni ‘ya su a dalilin shaye shayen miyagun kwayoyi.
Abu na uku, shi ne, irin hadin kan da gwamnatin Jihar Oyo take ba mu da al’ummomi da suke hanzarta ba mu labarin bullar irin wadannan mutane a maboyarsu.”
Mataimakin Gwamnan Jihar Oyo, Cif Moses Adeyemo, shi ne ya jagoranci kwamandodin tsaro daban-daban wajen cinna wuta ga tarin buhunan miyagun kwayoyi da aka kona su kurmus a cikin dajin kauyen Akilapa da ke kusa da birnin Ibadan.
Sarakuna da shugabannin kungiyoyi daban-daban ne suka halarci wajen wannan gangami na bana wanda wasu masana a kan harhada magunguna suka nuna wa dimbin mahalarta irin gwaje gwajen da suke yi domin tabbatar da cewa, miyagun kwayoyin na gaskiya ne. Irin wannan gwaji yana nuna launi daban daban na kowane nau’i na miyagun kwayoyin ne.
Na hudu daga hagu Mataimakin Gwamnan Jihar Oyo, Cif Moses Adeyemo ne ya jagoranci kwamandodin tsaro da suka cinna wuta ga miyagun kwayoyi da rundunar NDLEA ta kama a Jihar Oyo.