Hukumar NDLEA ta kama kayan maye a Ibadan
Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Oyo ta kama kananan jarkoki 30 da kwalabe 20 masu dauke da wani ruwan kayan maye mai suna “Skrushy” da ake sarrafa shi ta amfani da miyagun kwayoyi dangin Codeine da Tramadol da hodar Iblis da makamantansu. Kwamandan Hukumar, Misis Omolade Faboyede ce […]
Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Oyo ta kama kananan jarkoki 30 da kwalabe 20 masu dauke da wani ruwan kayan maye mai suna “Skrushy” da ake sarrafa shi ta amfani da miyagun kwayoyi dangin Codeine da Tramadol da hodar Iblis da makamantansu.
Kwamandan Hukumar, Misis Omolade Faboyede ce ta bayyana haka a takardar sanarwa da aka raba wa ’yan jarida a Ibadan dauke da sanya hannun Kakakin Hukumar, Misis Mutiat Okuwobi. Ta ce an yi kamen ne a ranar Lahadi lokacin wani samame da jami’anta suka kai cikin dare a wata mashaya da ke Unguwar Sango a Ibadan.
Hukumar ta ta ce, ta fara kai samamen ba-zata zuwa otal-otal da kulob-kulob ne bayan samun bayanan cewa matasa maza da mata suna amfani da wadannan wurare wajen shaye-shayen miyagun kwayoyi.
“Dirar mikiya na baya-baya da jami’an suka kai zuwa wani otal a Ibadan ya ba su damar kama miyagun allurai da kwayoyi da tukunyar shaken tabar Shisha da aka boye a cikin jakar mata,” inji sanarwar.
Sakamakon wani bincike da hukumar ta ce ta yi a kan matsalar shaye-shaye, ta ce ta gano cewa matasa maza da mata ne a kan gaba wajen kwankwadar wannan ruwan maye na “Skrushy” yayin da manyan mutane maza da mata suke biye da su.
Misis Faboyede ta ja kunnen gidajen sayar da barasa da kulob-kulob su janye jiki daga hada-hadar miyagun kwayoyi ko kuma a dauki matakin ladabtarwa a kansu. Ta roki kafofin labarai su taimaka wa hukumar da labarin bullar matattarar shaye-shayen abubuwan da suke lalata rayuwar matasa.
Idan ba a manta ba, a farkon bana ne Gwamnatin Jihar Oyo ta gudanar da aikin kamen mutane masu tabin hankali da ke kan tituna, inda aka kebe su a wani sansani da ake kula da lafiyarsu. A daidai wancan lokaci ne gwamnatin ta mika wadansu daga cikin wadannan mutane ga iyalansu bayan samun sauki. Amma binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa, yanzu haka irin wadannan mutane da aka mika su ga iyalansu sun dawo kan tituna inda ake ganinsu rike da tabar wiwi da sigari a hannu suna tsintar abinci a bola. Mafi yawancinsu matasa ne da ’yan mata da ake ganinsu da goyon kananan yara wadansu ma dauke da juna biyu.