Hukumar NDLEA ta kama masu ta’ammali da miyagun kwayoyi 221 a Bauchi
Hukumar Yaki da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Bauchi ta kama masu tu’ammali da miyagun kwayoyi 221, dauke da kilo 1,253 a bara. Hukumar ta ce hakan na nuna an samu raguwar aikata tu’ammali da miyagun kwayoyi sakamakon kama manyan dillalan tabar wiwi da sauran kaya masu sa maye a sassan jihar. Kwamandan […]
Hukumar Yaki da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Bauchi ta kama masu tu’ammali da miyagun kwayoyi 221, dauke da kilo 1,253 a bara. Hukumar ta ce hakan na nuna an samu raguwar aikata tu’ammali da miyagun kwayoyi sakamakon kama manyan dillalan tabar wiwi da sauran kaya masu sa maye a sassan jihar. Kwamandan Hukumar NDLEA ta Jihar Bauchi Mista Para Bawa Julius ne ya bayyana haka, inda ya ce an kai mutum 124 babbar kotu inda aka hukunta mutum 46 wasu 79 kuma aka gyara halayensu aka sallame su bayan sun yi alkawarin ba za su sake shiga wannan harka ba, yayin da mutum 18 kuma suke jiran hukunci. Mista Julius Bawa ya ce a bara sun kama motoci shida da babura 15 da ake aiki da su wajen raba miyagun kwayoyi a cibiyoyin sayar da su. “Haka kuma iyaye da dangi sun kawo mutum 75 don rike su saboda shigarsu cikin harkar miyagun kwayoyi kuma an gyara dabi’arsu yayin da aka koya wa mutum 27 sana’o’i da suka shafi aiki da na’ura mai kwakwalwa da dinki da kanikanci da gyaran ruwan famfo da sauran sana’o’i da ake koyarwa a hukumar,” inji shi. Ya ce ofishinsa ya samu nasarori masu yawa a bara inda suka kama manyan dillalan miyagun kwayoyi, kuma duk an kai su kotu an yi musu dauri mai tsanani kamar yadda doka ta tanada. Ya yaba wa gwamnatin jihar kan taimakon da take ba hukumar wajen yaki da da miyagun kwayoyi a jihar.