Hukumar NDLEA ta kame mai safarar miyagun kwayoyi
Hukumar Yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wani mai suna Ogochukwu Ogojie, mai sana’ar fiton kayayyaki daga Najeriya zuwa kasar waje yana kokarin fitar da sinadarin metapitamin, wanda ya fi hodar koken illa da kuma tsada a dukkan kasashen duniya.Ogochukwu ya zuba ruwan sinadarin ne cikin gallon din man gyada guda […]
Hukumar Yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wani mai suna Ogochukwu Ogojie, mai sana’ar fiton kayayyaki daga Najeriya zuwa kasar waje yana kokarin fitar da sinadarin metapitamin, wanda ya fi hodar koken illa da kuma tsada a dukkan kasashen duniya.
Ogochukwu ya zuba ruwan sinadarin ne cikin gallon din man gyada guda biyu, wanda yake yunkurin ganin an kai masa kasar Afirka ta Kudu, kuma ya kai wajen awon kayayyaki ne da sunan man gyada tare da sauran jarkokin man gyada.
Da yake wa taron manema labarai jawabi, shugaban hukumar na tashar jirgin saman Murtala Mohammed, Malam Hamza Umar ya ce nauyin ruwan sinadarin ya kai sama da kilogiran 7 da aka kiyasta ya kai na miliyoyin Naira, kuma wanda ake tuhumar ya tabbatar da nasa ne.
Malam Hamza ya ce Mista Ogochukwu ya tabbatar da cewa ya kwashe shekaru kusan 10 yana fiton kayayyaki a tashar jirgin saman, kuma shi ne ya sayi hajar domin ya dade yana aikin fiton kayayyaki, amma da kyar yake iya ciyar da kansa da kuma iyalansa.
Mista Ogochukwu, mai kimanin shekaru sama da 40, ya ce yana da mata da ’ya’ya 4, kuma ya amsa laifinsa, yana mai fadin rashin wadatar zuci da hadama ce ta tura shi ga wannan danyen aikin, alhalin yana sane da hukuncin da ka iya hawa kansa. Ya yi nadama domin idan an yanke masa hukuncin zaman gidan yari bai san wanda zai dauki dawainiyar iyalinsa ba.
Malam Hamza Umar ya ce da zarar sun kammala bincikensu, za su gurfanar da shi a kotu.