Hukumar NDLEA ta kame mai shekaru 61 da hodar koken

Jami’an yaki da safarar miyagun kwayoyi na kasa  da ke filin jirgin saman Murtala Mohammed  a birnin Ikko sun cafke  wani  dattijo mai shekaru 61 dauke da  hodar koken yana kokarin tsallakawa zuwa Istambul da ke kasar Turkiyya.Wannan dan taliki  da ya ce  sunansa Ogbodo Prince Ifenyi-chukwu, an kama shi ne sa’ilin bincike a  filin […]

Hukumar NDLEA ta kame mai shekaru 61 da hodar koken

Jami’an yaki da safarar miyagun kwayoyi na kasa  da ke filin jirgin saman Murtala Mohammed  a birnin Ikko sun cafke  wani  dattijo mai shekaru 61 dauke da  hodar koken yana kokarin tsallakawa zuwa Istambul da ke kasar Turkiyya.
Wannan dan taliki  da ya ce  sunansa Ogbodo Prince Ifenyi-chukwu, an kama shi ne sa’ilin bincike a  filin jirgin sama yayin da aka yanke gefen jikkarsa aka gano hodar mai nauyin kilogiram 1,250.
Da yake wa manema labarai jawabi, shugaban hukumar mai kula da tashar jirgin saman, Mallam Hamza Umar ya ce dattijon shi ne mai yawan shekarun da  hukumar ta kama tun farkon wannan shekarar.
Da ake binciken dattijon ko me ya kai shi shiga wannan harka, sai ya ce tsananin talauci ne, domin yana sayar da gas ne a kasuwar  Sabo Alaba, sai jalinsa ya karye kuma  ga shi da ’ya’ya da mata, ba wanda zai agaza masa.
Ya ce koken din na wasu ne suka aike shi da niyyar  ba shi ladar Dala dubu 5, sun ba shi Dala dubu 2, idan ya dawo su ba shi ciko, kuma su ne suka biya kudin tikitin jirginsa zuwa da dawowa.