Hukumar NDLEA ta kame wata mata da hodar iblis

Hukumar yaki da sha da safaran miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke Ikko ta cafke wata  mata mai suna A’isha Uwaminana, wadda  ta ce ta fito ne daga kasar Burundi ta shigo jirgin  AIR  REWANE  daga kasar Tanzaniya kuma ta  iso  nan  Najeriya  kafin saurayinta dan Najeriya  da  ta ce ya  ba ta  jikkar  da ke […]

Hukumar NDLEA ta kame wata mata da hodar iblis
Hukumar NDLEA ta kame wata mata da hodar iblis

Hukumar yaki da sha da safaran miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke Ikko ta cafke wata  mata mai suna A’isha Uwaminana, wadda  ta ce ta fito ne daga kasar Burundi ta shigo jirgin  AIR  REWANE  daga kasar Tanzaniya kuma ta  iso  nan  Najeriya  kafin saurayinta dan Najeriya  da  ta ce ya  ba ta  jikkar  da ke dauke da  wannan mugunyar  hajar  ya iso.
Hodar  ta iblis, wadda  ke  kunshe  cikin  jikkarta ta kaya,  ta ce saurayinta ne ya ba ta  kafin ya iso nan Najeriya, inda  za su  zo  domin bikin aurensu. Ta ce ta hadu da  wannan dan talikin ne  can kasarsu kuma  sun yi  alkawarin yin aure abin da ya sa  ya  fara  turo  ta zuwa Najeriya kafin shi ya iso, ta fara shirye-shiryen bikin auren nasu, sai dai ta ce ba ta da masaniyar  cewa  akwai  wannan  hodar  kunshe  cikin  wannan jikkar.
Kamar  yadda  shugaban hukumar  mai kula da  tashar jirgin saman Murtala  Mohammed,  Malam Hamza Umar  ya shaida wa wakilin Aminiya,  jirgin da matar ta shigo ba jirgi ne da aka saba  samun mutane dauke da  wannan hodar iblis  din.  Ya ce  yana ganin shigar ta jirgin wata  dabara  ce  ta  dauke  hankalin jami’an hukumar  domin ganin kila ba za a yi  wa fasinja  binciken kwakwaf ba, amma  ba ta san cewa  kowane  jirgi  ko fasinja  sai  an yi masa  binciken da ya dace.
Ya ce ba ita kadai ce ’yar kasan waje  da ke  hannun hukumar ba a yanzu  haka,  domin akwai  wasu biyar ’yan kasashe  biyar  da  hukumar ta  kame  cikin wannan shekarar  a lokutta  daban-daban kuma  akwai  wasu ukku  daban wadanda  su  har an yanke  musu hukunci  har  sun fara  zaman  gidan kaso.  Ya ce da  zarar sun kammala  binciken  wannan matar  za su  gurfanar da ita  gaban  kuliya.
Matar  ta ce wannan  shi ne karo na farko da ta zo Najeriya. Kamun matar ce a tashar jirgin saman Murtala  ya zo daidai da lokacin da wasu  jami’an kasar  Switzerland   masu yaki  da  harkoki  da miyagun kwayoyi na kasarsu suka zo domin duba  hanyoyin da  kasar  tasu  za ta  hada  kai da Najeriya  domin yakar wannan mummunar  sana’ar  tsakanin kasashen biyu  da ma  duniya  baki daya.
Da yake wa bakin nasa  marhabin, shugaban hukumar NDLEA  na kasa, Alhaji Ahmadu Giade  ya ce duk  da damke  masu  wannan mummunar  sana’ar  da  hukumar  ke yi  har  yanzu  wasu  ba su  daddara ba. Ya yi fata  za su yi  kyakkyawar  musayar  ra’ayi  da  bakin,  wanda  zai  amfani  kasashen biyu da ma sauran kasashen duniya.Ba a yi bayanin kowane  tsawon lokaci bakin jami’an za su yi a nan Najeriya ba.