Hukumar NDLEA ta nemi a hana shan giyar Goskolo a Jihar Filato
Hukumar Hana Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen Jihar Filato ta bukaci a samar da dokar da za ta hana shan giyar gargajiya irin su Goskolo da sauransu. Wani babban jami’i a hukumar Bello Mumini ya bayyana haka a lokacin taron wayar da kan jama’a kan illolin shan miyagun kwayoyin da […]
Hukumar Hana Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen Jihar Filato ta bukaci a samar da dokar da za ta hana shan giyar gargajiya irin su Goskolo da sauransu.
Wani babban jami’i a hukumar Bello Mumini ya bayyana haka a lokacin taron wayar da kan jama’a kan illolin shan miyagun kwayoyin da kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) da kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar suka shirya a Jos a ‘Ranar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta Duniya.’
Ya ce akwai wata giya mai suna Goskolo da ake hada ta a Jihar Filato da matasa da dama ba sa iya wuni ba tare da sun sha ta ba, inda take lalata rayuwar da yawa daga cikinsu.
Ya ce hukumarsu ba ta da damar yin dokar hana shan wannan giya, don haka ya bukaci gwamnatin Filato ta samar da dokar tun kafin matasan jihar su gama salwanta ta hanyar shan giyar Goskolo.
A lokacin da yake jawabi shugaban kungiyar NMA reshen jihar, Pokop W. Bupwatda ya ce za su ci gaba da shirya tarurruka irin wadannan don wayar da kan matasan jihar.
Shi ma shugaban kungiyar NUJ reshen jihar, Yakubu Taddy, wanda mataimakinsa Ben Mitu ya wakilta, ya ce, kungiyarsu za ta ci gaba da hada gwiwa da kungiyoyi daban-daban don kawo duk wani abu da zai taimaki al’ummar jihar da kasa baki daya.