Hukumar NDLEA ta nemi hadin kan kungiyar ECOWAS
Shugaban Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Kanar Muhammad Mustafa Abdullah (mai ritaya), ya nemi karin hadin kan kungiyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma (ECOWAS) domin kawar da safarar miyagun kwayoyi da wasu miyagun ayyuka a yankin. Kanar Mustafa Abdallah ya yi kiran ne a wurin taron hadin gwiwa kan […]

Shugaban Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Kanar Muhammad Mustafa Abdullah (mai ritaya), ya nemi karin hadin kan kungiyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma (ECOWAS) domin kawar da safarar miyagun kwayoyi da wasu miyagun ayyuka a yankin.
Kanar Mustafa Abdallah ya yi kiran ne a wurin taron hadin gwiwa kan horarwa na wuni 5 da kungiyar ECOWAS da hukumomin tsaro na yankin suka gudanar a iyakar Najeriya da Nijar na garin Ilelah da Kwanni da Rafin Duma.
Kanar Abdallah ya ce hukumarsa za ta yi tsayin daka wajen kawar da safarar miyagun kwayoyi a yankin musamman a kan iyakar Najeriya da Nijar da ake safarar miyagun kwayoyi da jabun magunguna, ta hanyar hada kai a tsakanin jami’anta da jami’an tsaro na Afirka ta Yamma.
Shugaban kungiyar ECOWAS, Mista Marcel de Souza wanda Mista Dieng Abdourahmane, Shugaban kula da tsaro a yankin kuma shugaban kwamitin ’yan sanda ya wakilta, ya ce yankin shi ne cibiyar safara da sha da samar da miyagun kwayoyin da sauran ayyukan batagari saboda rashin daukar matakan da suka dace a iyakokinsu na ruwa da kasa.
Wakilin Jamhuriyar a horarwa da aiki, Salifou Assoumane ya gode wa wadanda suka tsara shirin kuma ya roki a sanya hukumominsu a yakin.
Shugaban Tsaro na yankin wanda Mista Halidu Illo ya wakilta, ya ce sun fito da wani shiri mai suna NINIBO da yake fada da safarar miyagun kwayoyi da ayyukkan batagarin.