Hukumar NDLEA ta nemi masu bayar da gidajen haya su yi taka-tsantsan

Kwamandar Hukumar Yaki da Safarar Miyagun kwayoyi (NDLEA) ta Jihar Oyo, Uwargida Omolade Faboyede ta shawarci masu gidajen haya su sa ido tare da kyakkyawar lura da abubuwan da ke gudana cikin irin wadannan gidaje da suka bayar haya. Wannan shawara ta biyo bayan irin aikata miyagun ayyuka da wasu ke yi a cikin gidajen […]

Hukumar NDLEA ta nemi masu bayar da gidajen haya su yi taka-tsantsan

Kwamandar rundunar NDLEA ta Jihar Oyo ce Uwargida Omolade Faboyede yayin take nuna wa ’yan jarida tarin buhunan ganyen tabar wiwi da rundunar ta kama.Kwamandar Hukumar Yaki da Safarar Miyagun kwayoyi (NDLEA) ta Jihar Oyo, Uwargida Omolade Faboyede ta shawarci masu gidajen haya su sa ido tare da kyakkyawar lura da abubuwan da ke gudana cikin irin wadannan gidaje da suka bayar haya.
Wannan shawara ta biyo bayan irin aikata miyagun ayyuka da wasu ke yi a cikin gidajen suna tserewa, lamarin da ka iya kaiwa a kama masu gidajen da durkusar da su gaban kotu, saboda haka ta bukaci masu gidajen su rika bincike domin sanin yanayin mutanen da za su ba haya.
Wannan tsokaci, ya biyo bayan wani samame da rundunar ta gudanar ranar Juma’a a unguwar Alakia-Isebo da ke Ibadan, a inda ta gano buhunan tabar wiwi guda 396 da buhunan irin shuka na tabar guda 16 masu nauyin kilogiram 3,784.42 a cikin wani gida da wani mutumi ya karba haya yake hada-hadar kasuwancin wannan ganye a boye kafin asirinsa ya tonu.
Da take yi wa ’yan jarida bayani tare da nuna musu buhunan ganyen tabar wiwi da mutane 2 da rundunar ta kama, a ofishinta, Kwamanda Omolade ta ce duk da yake mutumin ya tsere, rundunar  ta yi nasarar kama matarsa ’yar shekaru 26 mai suna Blessing Jonathan da kanenta mai suna Biddof, mai shekaru 19.
Ta ce bincikensu ya nuna mai gidan bai san irin danyen aikin da ake kwabawa a gidan ba. “Amma muna ci gaba da bincike, idan muka gano cewa mai gidan yana sane, amma ya bayar da hayar gidan, shi ma za a kama shi a mika shi kotu domin yanke masa hukunci.” Inji ta.
Da yake karin haske, Mataimakin Kwamandan NDLEA a Jihar Oyo, Alhaji Isa Ibrahim ya ce, “Tun cikin watan Janairu wasu mutanen kirki suka ba mu labarin irin barnar da ake yi a cikin wannan gida, jami’anmu suka rika shawagi akai-akai, har muka kai ga wannan nasara. Muna kira ga jama’a su ba mu hadin kai da goyon baya domin gano maboyar irin wadannan miyagun abubuwa da suke lalata rayuwar matasa musamman.”