Hukumar NDLEA ta yi kamun farko a tashar jirgin saman Inugu

Ba a fi  wata  guda  ba da  fara  aiki  da  sabuwar  tashar jirgin sama  ta Akanu Ibiam da ke Inugu ba, a matsayin filin jirgin saman kasa da kasa ba,  Hukumar Yaki da Safarar Miyagun kwayoyi da Safararsu ta kasa (NDLEA) ta yi kamun farko  na  wani  wanda ya ce shi dalibi ne da hodar […]

Hukumar NDLEA ta yi kamun farko a tashar jirgin saman Inugu
Hukumar NDLEA ta yi kamun farko a tashar jirgin saman Inugu

Ba a fi  wata  guda  ba da  fara  aiki  da  sabuwar  tashar jirgin sama  ta Akanu Ibiam da ke Inugu ba, a matsayin filin jirgin saman kasa da kasa ba,  Hukumar Yaki da Safarar Miyagun kwayoyi da Safararsu ta kasa (NDLEA) ta yi kamun farko  na  wani  wanda ya ce shi dalibi ne da hodar koken ta  miliyoyin Naira.

dalibin mai suna Chizoba Anselem, wanda ya ce yana Jami’ar  Nnamdi Azikwe ne da ke garin Okar, an kama shi ne  a hanyarsa  ta zuwa kasar  Birazil  sa’ilin da  zai  shiga  jirgin  kamfanin Ethiopia,  wanda   zai yada  zango  a Dubai, bayan ya hadiye kullin koken 25 da  aka  nannade  cikin  kororon roba.
Da  yake wa  manema  labarai jawabi, shugaban hukumar na Inugu,  Mista Nsikak Abasi ya ce koken din na da nauyin kilogiram  1.25, wanda ke da kimar miliyoyin Naira kuma wanda ake tuhumar bai musa ba, ya ce an yi masa alkawarin Naira  dubu dari 5 ne.
Shi kuma  Francis Bawaba, wanda ke  zaune a Madrid  na kasar Spain an kama shi da koken, wadda nauyinta kilogiram 6.490 ne, wadda kumaaka kiyasta kudinta ya kai Naira miliyan 72 kuma  za a ba shi ladar Naira miliyan 3.3.
Shugaban hukumar, mai kula da tashar jirgin saman Murtala, Malam Hamza Umar  ya shaida wa manema  labarai  cewa da  zarar sun kammala  bincike za su  gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu.