Hukumar NDLEA ta yi nasarar cafke babban dillalin kwaya
Hukumar yaki da fatauci da tu’ammali da miyakun kwayoyi (NDLEA), ta kama Charles Onyenachi da ake zargin cewa hamshakin mai safarar miyakun kwayoyi ne a Kudu maso gabashin Najeriya. Mutumin, wanda ake wa lakani da Charles Taylor, tawagar jami’an tsaro na musamman ne suka kama shi a ranar Litinin da ta gabata, a wata turakar […]

Hukumar yaki da fatauci da tu’ammali da miyakun kwayoyi (NDLEA), ta kama Charles Onyenachi da ake zargin cewa hamshakin mai safarar miyakun kwayoyi ne a Kudu maso gabashin Najeriya.
Mutumin, wanda ake wa lakani da Charles Taylor, tawagar jami’an tsaro na musamman ne suka kama shi a ranar Litinin da ta gabata, a wata turakar boka da ke kauyen Ubakala, karamar Hukumar Umu’ahiya ta Kudu, Jihar Abiya.
Mai laifin, dan shekara hamsin, wanda ke da ’ya’ya uku, tun farko dai hukumar ta bayyana shelar nemansa tun shekara uku da ta gabata. Hukumar ta bayyana cewa a can baya, ta yi iyaka kokarinta iri daban-daban domin ganin ta kama shi amma abin ya faskara. A yanzu ma sun samu nasarar kama shi ne, a sakamakon bayanan sirri da suka samu.
Da yake magana da wakilinmu a inda yake tsare, Onyenachi ya ce ya fara wannan sana’a ta fataucin miyagun kwayoyi tun yana dan shekara 30 a duniya. Ya ce ya fara ne a matsayin dan aike a Jihar Delta, inda ya yi ta samun daukaka har ya kai ga shi ne babban mai gudanar da harkar a Kudu maso gabashin Najeriya gaba daya.
Da yake karin bayanin yadda ya soma sana’ar, ya ce a lokacin yana dan shekara 30, aikin kafinta ya fara koyo, inda abokin aikinsa ya shigar da shi sana’ar a matsayin dan aike, inda ake aikensa ya kai kwaya wurare daban-daban. Daga nan ya fara sayar da kullin tabar wiwi a kan Naira 20, kafin daga bisani harkar ta bunkasa.
“A yanzu kuwa a gida nake gudanar da sana’ar, wasu lokuta kuwa a dakunan otel, inda abokan huldata kan zo su same ni. Ina da abokan hulda iri daban-daban da suka hada da ’yan siyasa, har ma da fasto-fasto da ke gudanar da harkokinsu a sabbin coci-coci na zamani,” inji shi.
Da yake magana da wakilinmu dangane da nasarar kama hamshakin dillalin, Kwamandan hukumar na Jihar Abiya, Mista Akingbade Bamidele ya ce wannan babbar nasara ce da suka samu wajen yaki da safarar miyakun kwayoyi a Najeriya.