Hukumar NEAZDP tana samun nasara a Arewa maso Gabas
Babban Manajan Hukumar Bunkasa yankuna masu fama da fari da gusowar hamada a Arewa maso Gabas, North East Arid Zone Debelopment Programme (NEAZDP) da ke Jihar Yobe Dokta Hussain K. Hassan ya ce hukumar ta samu nasarar aiwatar da muhimman ayyuka sama da dubu 25 a shekara 26 da kafuwarta.Babban Manajan ya bayyana haka ne […]
Babban Manajan Hukumar Bunkasa yankuna masu fama da fari da gusowar hamada a Arewa maso Gabas, North East Arid Zone Debelopment Programme (NEAZDP) da ke Jihar Yobe Dokta Hussain K. Hassan ya ce hukumar ta samu nasarar aiwatar da muhimman ayyuka sama da dubu 25 a shekara 26 da kafuwarta.
Babban Manajan ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya a ofishinsa da ke Garin Alkali, inda ya ce, ayyukan da suka yi sun hada da gina kananan makarantun kula da noman rani da damina da kiwon lafiya da samar da bunkasa kananan sana’o’i na dogaro da kai ga mata da matasa tare da dakile gusowar hamada.
Manajan ya ce an kafa Hukumar NEAZDP ne bisa ga wani shiri na Tarayyar Turai na ba da tallafi ga kasashe masu fama da karancin ruwan sama a 1988 a Lome ta kasar Togo, kuma yankin Arewa maso Gabas, musamman tsohuwar Jihar Borno na da irin wannan matsala, kuma ya ce shirin ya fara aiki
ne a 1990, bisa hadin gwiwar da Tarayyar Turai da Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno. Ya ce, lokacin da aka kirkiro Jihar Yobe a 1991 sai cibiyar hukumar ta kasance a cikinta.
Ya ce muhimman ayyukan da cibiyar ta fi karkata a kansu su ne bunkasa yankunan karkara wajen samar da wadataccen ruwan sha da kiwon dabbobi da kamun kifi ko noman rani ta hanyar gina kananan
madatsun ruwa da rainon itatuwa masu nuna da wuri da makamantansu tare da raba wa matan karkara jari don gudanar da kananan sana’o’i domin dogaro da kansu.
Dokta Hussein ya ce a tsawon zaman da ya yi a cibiyar sun yi ayyuka sama da dubu 10, ciki har da rainon itatuwan dashwe sama da dubu 200 a kowacce shekara tare rarraba su ga jama’a domin dasawa a gonaki da gidajensu da kuma makarantu kyauta.
Ya ce hukumar ta dasa itatuwa a hanyar Bayamari zuwa Damaturu masu tsawon kilomita daya da fili mai kadada goma a Bukartin-Gabas tare da tallafa wa shirin Gwamnatin Tarayya na dashen itatuwa daga Zamfara zuwa Borno mai tsawon kilomita 1500, inda ta ba da kyautar itatuwa kimanin dubu 50 don yaki da kwararowar hamada.