Hukumar NEMA ta nemi direbobi su yi taka-tsantsan da tuki a karshen shekara

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) shiyyar jihohin Bauchi da Gombe da Taraba ta gudanar da taron ilimantar da direbobi da sauran jama’a kan yadda za su gudanar da zirga-zirgar a watannin karshen shekara don kare rayuka da dukiyoyinsu.Hukumar da hadin gwiwar Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC) da sauran masu ruwa da tsaki […]

Hukumar NEMA ta nemi direbobi su yi taka-tsantsan da tuki a karshen shekara

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) shiyyar jihohin Bauchi da Gombe da Taraba ta gudanar da taron ilimantar da direbobi da sauran jama’a kan yadda za su gudanar da zirga-zirgar a watannin karshen shekara don kare rayuka da dukiyoyinsu.
Hukumar da hadin gwiwar Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC) da sauran masu ruwa da tsaki sun kuma nuna wa jama’a a zahiri kan yadda za a rage aukuwar hadurra a watannin karshen shekara da kuma yadda za a bayar da taimako tare da ceto rayukan wadanda hadari ya rutsa da su a cikin gaggawa.
Kakakin Hukumar NEMA Umar Shitu Madigawa ya kara wa wakilinmu bayani game da wannan aiki da ya ce an gudanar da shi ne a karkashin darakta mai lura da shiyyar Mista Apolos Jedial, inda ya ce sun fito da tsarin nuna wa mutane yadda hadari ke aukuwa da kuma yadda za a ceto mutanen da lamarin ya shafa ta hanyar aiki da wasu kayayyaki na balle abubuwan hawa domin ciro mutanen da suka makale a lokacin da hadari ya auku.
Umar Madigawa, ya ce suna wayar da kan jama’a ne don su rage gudu da tukin ganganci a tsakanin direbobi ta yadda za su kasance masu lura da hakuri da bin ka’idojin tuki.
“Don haka muka horar da mutane game da yadda za a samu nasarar lura da rayuwa da kiyaye dokokin hanya da kuma rage gudu da kula da lafiyar abin hawa,” inji shi.
Bayan gama taron Hukumar NEMA ta bayar da tallafin kayayyaki tirela biyu don raba wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a bara da suka hada da na abinci da kayan amfanin yau da kullum. Ya ce sun je sun duba irin barnar da aka samu da kuma rubuta kayan da ake bukata na gini da na ayyukan gida da na abinci kuma takwarar hukumar ta Jihar Bauchi (SEMA) ta yi alkawarin isar da kayan a ga kowane mutum kuma su ma za su halarci wannan wurin rabon.