Hukumar NEMA za ta fadada sansanin ’yan gudun hijira zuwa garin Maiduguri

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) a shiyyar Arewa maso Gabas, ta ce za ta fadada sansanin ’yan gudun hijira zuwa garin Maiduguri, ta yadda za a iya taimaka wa wadanda hare-haren Boko Haram ke shafa a cikin gaggawa.Wani babban jami’i a hukumar Malam Muhammed Kanar ne ya fada wa wakilinmu haka a […]

Hukumar NEMA za ta fadada sansanin ’yan gudun hijira zuwa garin Maiduguri
Hukumar NEMA za ta fadada sansanin ’yan gudun hijira zuwa garin Maiduguri

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) a shiyyar Arewa maso Gabas, ta ce za ta fadada sansanin ’yan gudun hijira zuwa garin Maiduguri, ta yadda za a iya taimaka wa wadanda hare-haren Boko Haram ke shafa a cikin gaggawa.
Wani babban jami’i a hukumar Malam Muhammed Kanar ne ya fada wa wakilinmu haka a garin Maiduguri.
Malam Muhammed Kanar ya ce “Saboda matsanancin halin da mutane ke shiga na rashin abinci da matsuguni da kuma tsoron kada mahara su auka musu da kuma yawan wadanda aka auka musu da ke bukatar abinci da matsuguni ne ya suke tunanin bude wani katafaren sansanin ’yan gudun hijira a garin Maiduguri bayan sun kammala gudanar da aikin tantance yawan mutanen da ke bukatar taimako, ta yadda hukumar za ta samu saukin gudanar da ayyukanta.
Ya ce suna samun wasu ’yan matsaloli nan da can, to amma a yanzu hukumar ta yi rajistar ’yan gudun hijira dubu 120 wadanda suka fito daga kauyuka 4 da suka hada da Yawuri da Mainari da Modumari da Gumbari a karamar Hukumar Konduga da yanzu haka suke gudun hijira a Makarantar Firamare ta Rukunin Gidaje na Dalori.
Jami’in ya ce yanzu haka yara da mata da tsofaffi da suka bar gidaje da garuruwansu saboda matsalar hare-haren ’yan Boko Haram.
A wata sabuwa kuma kungiyar Boko Haram ta sake kai hari a wani kauye kusa da Chibok, inda suka kashe mutum biyar suka kuma yi awon gaba da kayan abinci. Bayanai sun ce ’yan bindigar sun kai harin ne a kauyuka biyu cikin daren ranar Litinin wato kauyen Tohya da Wurojene masu tazarar kilomita 13 da 14 daga Chibok, inda suka kone mafi yawan gidaje da kasuwanni. Wannan hari ya zo ne kasa da mako guda da sace wasu matan Fulani sama da 20 da ake zaton ’yan bindigar suka yi a yankin, kamar dai yadda wani shugaban al’mmar kauyen Tohya mai suna Zamani Ema, ya tabbatar wa wakilinmu. “Su ’yan bindigar sun zo kauyen ne wajen karfe 7:00 na yamma suka bude wa mutane wuta inda mu kuma muka gudu zuwa cikin daji da safe sai muka tarar cewa sun kone kauyukan Tohya da Wurojene, inda kuma suka kashe mutum biyar,” inji shi.