Hukumar NEMA za ta tsugunar da sama da mutum dubu 100 a jihohi uku

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) za ta tsugunar da sama da mutum dubu 100 da ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu a jihohin Bauchi da Gombe da Taraba. Shugaban Hukumar NEMA Alhaji Mohammed Sani Sidi ne ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyarar aiki Jihar Bauchi inda ya kaddamar da sansanin […]

Hukumar NEMA za ta tsugunar da sama da mutum dubu 100 a jihohi uku

Shugaban hukumar NEMA, Alhaji Sani Sidi a KirfiHukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) za ta tsugunar da sama da mutum dubu 100 da ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu a jihohin Bauchi da Gombe da Taraba. Shugaban Hukumar NEMA Alhaji Mohammed Sani Sidi ne ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyarar aiki Jihar Bauchi inda ya kaddamar da sansanin farko a garin Kirfi da za a lura da mutanen Bauchi ta Kudu da ruwa ya raba da gidajensu. Ya ce an samar da dakunan kwanan maza daban na mata daban da magewayi da makaranta da wurin dafa abinci da dakin ajiye kaya da asibiti da rijiyar burtsatse a matsugunin, kuma za a ba da abinci ga wadanda aka tsugunar a sansanonin har lokacin da za su samu taimakon gwamnati. Alhaji Sani Sidi ya ce sama da mutum milyan biyu ruwa ya tagayyara a sassan kasar nan a bara, wannan ya sa lokacin da Hukumar Kula da Yanayi ta kasa (NAMEIT) ta ce a bana za a sake samun ambaliyar ruwa, sai Shugaba Goodluck Jonathan ya shirya kwamitin musamman don shirya yadda za a gina sansanonin tsugunar da mutanen da suka samu kansu a cikin wannan matsala. Ya ce za a gina sansanonin a kowane sashin kasar nan da ake zaton ambaliyar za ta auku. Ya ce saboda Jihar Bauchi ta fi rinjayen wadanda ambaliyar ta tagayyara, ya sa aka fara da ginsa sansanin a garin Kirfi inda za a tsugunar da mutum 5,700, sai Kore a yankin Gamawa mutum dubu 13, sai Ningi inda za a tsugunar da mutum dubu 11. Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Sagir Aminu Saleh wanda ya karbi Daraktan na NEMA, ya ce hukumar ta bayar da taimakon dubban buhunnan gero da dawo da masara da kayan shayi da sukari da zannuwa da man girki da katifu da barguna da sauransu.