Hukumar NEPC za ta samar da ayyukan yi dubu 6 daga kasuwancin kashu
Hukumar Bunkasa Harkokin Fita da Kayayyaki ta Najeriya (NEPC), ta ce za ta samar da ayyukan yi dubu 6 daga sana’ar sarrafawa da cinikin ’ya’yan yazawa (kashu) inda masu cin gajiyar haka za su kasance kashi 80 cikin 100 mata ne, domin inganta rayuwarsu da samar da karin abincin a kasa. Babban Darakan Hukumar NEPC, […]
Hukumar Bunkasa Harkokin Fita da Kayayyaki ta Najeriya (NEPC), ta ce za ta samar da ayyukan yi dubu 6 daga sana’ar sarrafawa da cinikin ’ya’yan yazawa (kashu) inda masu cin gajiyar haka za su kasance kashi 80 cikin 100 mata ne, domin inganta rayuwarsu da samar da karin abincin a kasa.
Babban Darakan Hukumar NEPC, Abdullahi Sidi Aliyu ne ya bayyana haka a yayin gudanar da wata bita ta wuni daya da hukumar ta shirya don bai wa mahalarta horo kan muhimmanci da yadda ake sarrafa ’ya’yan yazawa da koko da ridi don inganta rayuwar jama’a. Ya ce wannan shiri zai kawo ci gaban kasuwanci da kuma tallafa wa kananan ’yan kasuwa.
Haka zalika Hukumar ta NEPC na aiki tukuru tare da hadin gwiwar cibiyoyin bunkasa harkokin fita da kayayyaki zuwa kasashen ketare, kuma za gina farfajiyar kwararru wanda za ta ba da damar kutsawa cikin kasuwar Tarayyar Turai.
Ita ma Mataimakiyar Babban Daraktan, Misis Ebelyn Obidike ta ce, “Kimanin tan dubu 150 da ake samarwa daga noma da samar da yazawa, tan dubu15 ne kacal ake sarrafawa a nan gida Najeriya wanda yake nuni da kashi 10 kacal cikin 100,” inji ta.