Hukumar NOA ta gudanar da taron wayar da kan jama’a
Hukumar wayar da kan jama’a (National Orientation Agency (NOA) ta gudanar da taron bita don wayar da kan ’yan Arewa kan muhimmancin dokar neman bayanin ayyukan gwamnati (Freedon of Information Act).Babban jami’in hukumar na karamar Hukumar Amuwo Odofin da ke Jihar Legas, Mista Titus T. Daodu ya bayyana wa Aminiya cewa hukumar ta shirya taron […]

Hukumar wayar da kan jama’a (National Orientation Agency (NOA) ta gudanar da taron bita don wayar da kan ’yan Arewa kan muhimmancin dokar neman bayanin ayyukan gwamnati (Freedon of Information Act).
Babban jami’in hukumar na karamar Hukumar Amuwo Odofin da ke Jihar Legas, Mista Titus T. Daodu ya bayyana wa Aminiya cewa hukumar ta shirya taron ne saboda la’akari da ta yi na yadda mutane ba su damu da sanin abin da gwamnati take yi ba.
Ya ce, “Irin halin ko-in-kula da mutanenmu ke nunawa wajen sanin bayanin abubuwan da gwamnati ke yi, ya sa wasu bata-garin shugabanni ke yin abin da suka ga dama da dukiyar jama’a. Shi ya sa muka kira wannan taro don mu wayar da kan mutanenmu su san ’yancin da suke da shi na sanin abin da gwamnati take yi. Muna so mutane su gane cewa dokar samun bayani, wacce shugaban kasa ya sanya wa hannu a shekarar 2011, ta ba su damar su je duk wata ma’akata tun daga karamar hukuma da gwamnatin jiha har zuwa ta tarayya su nemi bayani kan al’amura da ayyukan gwamnati”.
Ya ci gaba da cewa a yanzu duk wata ma’akata ko wani bangare na gwamnati da ya ki ba da bayanin da aka nema, ya saba wa doka. Saboda haka dole ma’aikata ko ta gwamnati da mai zaman kanta ta rika ajiye bayanai don jama’a. Kuma dole kowace ma’aikata ta fitar da ofishi wanda zai rika lura da bayanan ma’aikatar.
Ya ce hukumar ta shirya taron a jihohi bakwai na kasar nan har da Jihar Legas.
Da yake jawabi, sarkin Hausawan FASTAC, Alhaji Umaru Yunusa, ya bayyana farin cikinsa da yadda hukumar NOA ta tuna da ’yan Arewa har ta shirya musu taro don wayar da kansu.
Alhaji Umaru ya yi alkawarin ci gaba da ba hukumar goyon baya duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Shugaban kungiyar Arewa Initiatibe for balue Adbancement and Adbocacy, wadda ke wayar da kan jama’a, Aliyu Ibrahim ya bayyana cewa muhimmancin taron shi ya sa kungiyarsu ta ga ya dace ta hada gwiwa da hukumar NOA don cimma nasarar shirin.
Ya bayyana cewa kungiyarsu a shirye take duk lokacin da hukumar NOA ta nemi gudunmawarta ta ba ta goyon baya da hadin kai.