Hukumar NPA ta kai dauki ga ’yan gudun hijirar Yobe

Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa ta Najeriya (NPA) ta kai kayan tallafi ga gwamnatin Jihar Yobe don mika su ga ’yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya tilasta musu barin garuruwansu a jihar.Da ya ke karbar jami’an hukumar ta NPA Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce babu sauran wata karamar hukuma a jihar […]

Hukumar NPA ta kai dauki ga ’yan gudun hijirar Yobe
Hukumar NPA ta kai dauki ga ’yan gudun hijirar Yobe

Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa ta Najeriya (NPA) ta kai kayan tallafi ga gwamnatin Jihar Yobe don mika su ga ’yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya tilasta musu barin garuruwansu a jihar.
Da ya ke karbar jami’an hukumar ta NPA Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce babu sauran wata karamar hukuma a jihar da ta rage a hannun ’yan Boko Haram a yanzu.
Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Baba Malam Wali ya wakilta ya ce duk yankunan da a baya ’yan Boko Haram ke rike da su wato Gujba da Gulani a halin da ake ciki rundunar sojoji da ke aikin dawo da zaman lafiya a jihar sun ’yanto su.
Gwamnan ya ce babban abin da ya rage a gaban gwamnatin shi ne yadda za a tsara hanyoyin mayar da ’yan gudun hijirar zuwa garuruwansu.
Ya ce, a yanzu haka jihar na da ’yan gudun hijira kimanin dubu 300, kuma cikin wannan adadi mutum dubu 100 ne ke zaune a sansanonin da aka tanada, yayin da sauran kuma ke zaune ne tare da jama’ar gari.
Ya yaba wa Hukumar NPA kan samar da wannan tallafi, inda ya ba da tabbacin cewaza a raba kayayyakin ga wadanda suka cancanta a ba su.
Tun farko jagoran tawagar, Malam Isa Suwaid ya ce, hukumarsu ta NPA ta kawo tallafin ne ga ’yan gudun hijirar domin rage musu radadin rayuwa.
Daga cikin kayayyakin akwai buhunan gero 100 da na masara 100 da jarkunan man girki 150 da katifu 150 da tabarmi 1,500 da kuma barguna 500 da sauransu.