Hukumar NSC ta tunkari masu gudanar da ayyuka kan korafe-korafen masu jiragen ruwa

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), a matsayinta na mai tsara harkokin tattalin arziki a tashoshin ruwa tana warware korafe-korafe da dama da masu shigo da kaya da dillalansu na Kwastam suke kawowa game da nasu gudanar da ayyuka a tashohsin. korafe-korafen, kamar yadda Hukumar NSC ta gano sun shafi zargin da […]

Hukumar NSC ta tunkari masu gudanar da ayyuka kan korafe-korafen masu jiragen ruwa

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), a matsayinta na mai tsara harkokin tattalin arziki a tashoshin ruwa tana warware korafe-korafe da dama da masu shigo da kaya da dillalansu na Kwastam suke kawowa game da nasu gudanar da ayyuka a tashohsin.

korafe-korafen, kamar yadda Hukumar NSC ta gano sun shafi zargin da ake yi wa wasu kamfanonin jiragen ruwa da masu gudanar da tashoshin tsayuwar jiragen da suke kawo nakasu a harkoki a tasoshin ruwan.

Wata majiya a sashen karbar korafi na Hukumar NSC, ta ce, wasu daga cikin matsalolin da aka magance sun hada da mugun karin kudin da ake caza da kudin da ake karba a gefen wuraren tsayawar jiragen da ake ganin karbar haraji ne rubi-rubi da karbar kudin sauya wa kaya wuri ba tare da tuntubar masu shigo da kayayyakin ba da kuma karya yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin kamfanonin jiragen ruwa da wadanda suka dauko shatarsu.

Yarjejeniyar dauko kayayyakin tana gudana ce a tsakanin mamallakin jirgin ruwa da wani (da ake kira mai daukar shata), inda a ciki mai jirgin ruwan zai amince ya dauko kaya a madadin wanda ya dauko shata a cikin jirgin, ko ya bai wa mai shatar daukacin jirgin ya yi amfani da shi ko wani bangare na jirgin dakon kayan domin dauko kayayyakinsa na wani lokaci.

Sauran sun hada da rashin kyakkyawar dangantaka da dillalan Kwastam suka bayyana da cin zarafi da wulakanta kayayyakin da suka kawo da masu fitar da kaya da dillalai masu tantance kaya daga kamfanonin jiragen ruwa da jami’an tsaron da suke tudun da ake sauke kayayyakin ke yi.

Sauran matsalolin da ake korafi a kansu akwai rashin tsari wajen lodin kaya, wadda hakan ke jawo matsar kai kwantainoni inda za a daddale a auna su, sai kuma lalata jiragen dakon kayan da ake yi a tashoshin ruwan da wuraren sauke kaya da sito-sito da bacewar kaya yayin sauke su ko kai su ga masu su da jan kafa wajen karbar kwantainonin da ake sauke kayayyakinsu daga kamfanonin jiragen ruwa da suke wasu wuraren sauke kayayyakin ko cinkoso da kuma asarar jirgin ruwan dakon kaya.

Har ila yau ana zargin wasu kamfanonin jiragen ruwa da rashin maido da kudaden da aka biya na jinginar kwatainonin da ba su dauke da kaya da kuma rashin mai da sauran kudin hayar da aka biya da ya wuce kima. 

Wani abin aka bayyana yana ci wa masu hakar tuwo a kwarya shi ne karbar kudaden da suka wuce kima kuma mabambanta daga wasu wuraren tsayuwar jiragen ruwa a bakin gaba.

Irin wadannan abokan harka a tashoshin ruwan an ce suna kai kuka ga Hukumar NSC domin ta sanya baki ne bayan kokrinsu na ganin masu gudanar da ayyukan sun magance matsalolin ya ci tura.

Bayanai sun ce hukumar tana ganawa a kai-a-kai da masu gudanar da ayyukan da lamarin ya shafa a kokarin da take yi na magance korafe-korafen. Wasu daga cikin matsalolin da aka kawo a yayin ganawar tuni an shawo kansu, yayin da hukumar ke ci gaba ta tattaunawa da masu gudanar da ayyukan da lamarin ya shafa, tana matsa musu a inda ya dace domin su yi abin da ya kamata.

Majiyar ta ce hukumar tana lallama ce,kuma tana daukar matakai masu zafi ne kawai a inda masu gudanar da ayyukan suka gaza bin hanyar lumana.

Shugaban kungiyar Masu Dakon Kaya a Tasoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NAGAFF), Cif Increase Uche ya bayyana jin dadinsa game da matakan da Hukumar NSC ta dauka na wasu ayyuka da tsare-tsare, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen saukaka hada-hada a tasoshin jiragen ruwan kasar nan.